Gwamnatin jihar Kano ta yi Allah wadai da kakkausar murya kan ta’addancin da ‘ya’yan jam’iyyar NNPP suka yi a jihar yayin kaddamar da ofishin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a Sharada dake cikin babban birnin jihar.
A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai kuma mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben Gawuna/Garo Malam Muhammad Garba ya fitar, ya bayyana cewa a yayin da gwamnati ke tabbatar da daidaito wajen yakin neman zabe na dukkan jam’iyyun siyasa, abin takaici ne yadda jam’iyyar NNPP ta fara kai hari ga jama’ar da basu ji basu gani ba.
Ya ce, ya kamata taron a gudanar da shi cikin lumana, amma, ‘ya’yan jam’iyyar sai suka yi amfani da muggan makamai suka maida taron wajen farmakar mazauna yankin, lamarin da ya yi sanadin mutuwar wasu da kuma sace wayoyin salular wadanda basu ji basu gani ba.
Malam Garba ya kara da cewa, gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta yi matukar mamakin yadda taron siyasa ya koma na kwace, da alama akwai wani shiri da jam’iyyar NNPP ke yi na kokarin wargaza yanayin siyasar zaman lafiyar da ake yi a jihar.
Kwamishinan ya bayyana cewa Gwamna Ganduje ya nemi jami’an tsaro da su ci gaba da gudanar da ayyukansu ta hanyar tabbatar da cewa duk wani gangamin siyasa an gudanar da shi cikin kwanciyar hankali tare da tunkarar duk wani mutum ko kungiyar da ta kuduri aniyar haifar da hargitsi.