Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kai ziyarar jajantawa zuwa wurin da wani gini mai hawa uku ya ruguzo a yankin da ake gudanar da harkokin kasuwanci da ke titin Beirut a Jihar Kano.
Daraktan yada labaran Mataimakin Gwamna, Hassan Musa Fagge ya shaida wa LEADERSHIP Hausa cewa Gwamnan wanda mataimakinsa, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya wakilta ya bayyana hadarin da cewa wata annoba ce.
- ‘Yan Bindiga Sun Yi Wa Sojoji Kwanton Bauna, Sun Kashe Sojoji 2 A Katsina
- An Kashe ‘Yan Boko Haram 49 A Sansaninsu 3 Yayin Luguden Wuta Ta Sama
Ya ce Gwamnatin Jihar Kano za ta gudanar da cikakken bincike domin gano dalilin ruguzowar ginin.
Haka kuma gwamnan ya bukaci jama’a da su kaurace wa wurin domin bayar da dama ga tawagar masu kawo dauki da injiniyoyi da ke karkashin kulawa ma’aikatar ayyuka su ci gaba da bincike domin ceto wadanda hadarin ya rutsa da su.
Hakazalika, ya nuna farin cikinsa bisa yadda wasu kamfanoni gine-gine da sauran cibiyoyin ba da agajin gaggawa suka taimaka wajen ceto mutanen da rugujewar ginin ya rutsa da su.