ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Bikin Ranar Hausa Ya Gudana A Nijeriya Da Wasu Kasashen Duniya

by Mustapha Ibrahim
4 years ago
Ranar Hausa

An dai ware ranar 26 ga watan Agusta na kowacce shekara ta kasance ranar bikin Hausa ta duniya, rana ce da ta samo asali tun a shekarar 1910 daga wani Bature wanda ya kirkiri harafin K,D,B,da kalmar KWA, KYA da sauransu.

An sake habaka bikin a ‘yan shekarun nan ta hanyar tunawa da ranar a shafukan sada zumunta.

  • ‘Yan Bindiga Sun Yi Wa Sojoji Kwanton Bauna, Sun Kashe Sojoji 2 A Katsina
  • Ma’aikatan Gwamnati Sun Fi ‘Yan Siyasa Cin Hanci Da Rashawa – Kwamitin Majalisar Dattawa

Bayanai sun tabbatar da cewa an fara gudanar da wannan biki tun shekaru 100 da suka gabata, inda a yanzu ake gudanarwa a duk fadin duniya wanda yake nuna cewa, Hausa harshe ne mai albarka da karbuwa a duniya kamar dai yadda bikin ke nunuwa.

ADVERTISEMENT

A Kano, Kungiyar Marubuta ta shirya bikin ranar ne a Makarantar Nazarin Harshen Larbci da Shari’a ta Malam Aminu Kano a ranar Juma’ar da ta gabata da kuma wasu ranaku, saboda bunkasa wannan rana.

Da yake jawabi a wurin bikin, Sarkin Hausawan Afirka kuma Sardauna Agadaz, Dakta Abdulkadir Labaran Koguna ya bayyana cewa albarkar harshen Hausa ya sa babu wani harshe da yake da haruffa a Nijeriya ko ma a wasu kasashen da za a iya rubuta alkur’ani mai girma cikin sauki kamar sa.

LABARAI MASU NASABA

Ko Yakin Iran Zai Kawo Karshen Kawancen Amurka Da Kasashen Larabawa?

Yadda Sauya Shekar ‘Yan Siyasa Ta Sauya Fasalin Majalisar Dokokin Kasa

Ya ce sauran harsuna kamar Yoruba, Ibo, Fulatanci da makamantansu suna da wuya wajen rubuta alkur’ani mai girma da su, domin a Hausa ne ake da alu, anbaki, alikafa irin na Larabci kuma ko ma wajen rera karatun kur’ani in aka saurari Yarabawa za ka ga ya sha bamban, saboda ba su da harufa kamar yadda Hausa take da su.

Rahotanni sun bayyana cewa an gudanar da bukukuwan ranar Hausa ta duniya a dukkan jihohin Nijeriya guda 36 ciki har da Abuja.

A Jihar Kano, an gudanar da bikin a fadar Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, inda aka gwangwaje da bayanan ranar Hausa da kuma karbar bakuncin kungiyoyi masu alaka da Hausa daga jihohin Gombe, Zamfara wadanda suka halarci taron na fadar Sarkin Kano a ranar Juma’ar da ta gabata.

Haka ma a fadar Mai Martaba Sarkin Dutse, Alhaji Nuhu Muhammadu Sanusi, da ke Jihar Jigawa an yi kasaitaccen biki, inda aka fadada Daular Sarkin Hausawan Afirka ta hanyar nada sarautu 7 na sarkin Hausawa a Nijeriya, wanda aka nada Alhaji Munir na Kura a matsayin Galadiman Sarkin Hausawa na Jamhuriyar Benin, sai sarkin Hausawan Sudan da aka nada Alhaji Shamsudeen da sarkin wakar Hausawan Afirka, Alhaji Sani Kaka Dawa, da dai sauran masarautu ga masu kishin harshen Hausa da kuma al’adunsu.

Hakazalika, an gudanar da bikin na ranar Hausa a kasashe 49 cikin kasashe 59 na Nahiyar Afrika da ake da su da wasu kasashe da ke kan tsuburi.

Haka kuma bikin ya gudana a manyan kasashe irin su Saudiyya, China, Amurka, Faransa, da sauran su.

A dai cikin jawabin Sarkin Hausawan Afirka, Dakta Abdulkadir Labaran Koguna ya ce “Daukakar Hausa a duniyarmu ta yau ya sa a 2019, Hausa ta zama harshe na 13 a duniya, amma yanzu za ka samu Hausa a mataki na 9 ko na 8 a duniya.

“Yanzu Hausa ita ce harshen na 4 da ake fadakar da mutane da shi a wajen jifan Shedan a wurin a aikin Hajji a kasar Saudiyya.

A shekaru 3 da suka wuce kuma Hausa ce harshe na 7 cikin harsuna 9 da ake fassara huduba a Masallacin Harami a aikin Hajji a shekarun da suka gabata.

Harshen Hausa ya samu daukaka da dama a duniya.” Har ila yau, Dakta Koguna ya warware zare da abawa a kan munakisar da ake kokarin kitsawa don haddasa sabuwar gaba a tsakanin Hausawa da Fulani dangane da Jihadin Shehu Usman Danfodiyo.

“Kishin Hausa muke yi ba maguzancin da Shehu Usman Danfodiyo ya yaka ba, wani sabon makirci da muka lura ya bullo shi ne, cusa kiyayyar Fulani a zukatan Hausawa da kuma cusa kiyayyar Hausawa ga Fulani, musamman tarihin karyar da ake yadawa na cewa Shehu Usman Danfodiyo ya yaki Hausawa, sannan ya kafa Daular Fulani.

Wannan makirci ne babba a lura da shi tare da yin hattara, saboda ana amfani da ‘yan daban Hausa wajen afka wa Fulani sakamakon wannan makirci.

Haka kuma ana amfani da ‘yan daban Fulani wajen afka wa Hausawa tare da aibata Danfodiyo wai ya kau da al’adun Hausawa na tarihi.

“Danfodiyo al’adun maguzanci ya kawar ya kawo na musulunci, kuma musulunci ne gaba da Hausa da Fulantaci, aibata Danfodiyo maguzanci ne kuma makirci ne daga makiyanmu na nesa da na kusa, ya kamata a yi hattara da irin wadannan abubuwa.”

Shi ma Sarkin Hausawan Tukulmawa da ke Jihar Gombe, Alhaji Ibrahim Haruna, wanda har ila yau shi ne shugaban Kungiyar Arewanmu Duniyarmu da ta hada harsuna da kabilun arewa kaf, mai shalkwata a Kaduna, ya tofa albarkacin bakinsa a lokacin kungiyoyi suka gabatar da jawabai a ranar Hausar a fadar Mai Martaba Sarkin Kano.

Tukulmawa ya ce kungiyarsu ta hada kan kabilun arewa, wanda Hausawa ne kan gaba kuma aikinta shi ne fahimtar juna da samar da hadin kai, tsaro, yakar zalunci ba tare da la’akari da addini ko harshe ba.

A cewarsa, akwai wani sashi na shugabanci a wannan kungiya wanda ya kunshi Malaman Musulunci da na Kirista domin cimma burinmu na ceton arewa da Nijeriya baki daya.

Ya kara da cewa a cikin malaman Musulunci na wannan kungiyar akwai Sheik Adam Mai Hula, Sheik Sambo Rigacikum, sai kuma Fasto Yohana Buru, Rabaran Abarakallah, shugaban CAN na arewa.

Shi kuwa Gafakan Gombe, Alhaji Musa Ahmad Muhammad ya yi kira ne a yi amfani da ranar Hausa ta duniya wajen yi wa Nijeriya addu’a ta samun tsaro da zaman lafiya.

Ita kuwa shugabar mata da matasa daga jihar Zamfara, Hajiya Fatima ta ce su mata za su dage wajen raya al’adun Hausawa ta hanyar saka sutura a ko ina fadin duniya.

Dakta Hassan Sulaiman Kofar Naisa, masani kuma tsohon ma’aikacin fadar shugaban kasa da ya yi ritaya, ya ce Hausawa na sahun gaba wajen kyawawan al’adu da dabi’u masu kyau a duniya.

“Mu Hausawa muna da zumunci, kunya, kara, saukin kai, tawali’u, rikon alkawari, sanin ya kamata da sauran su. Duk Bahaushen asali yana alfahari da wadannan al’adu da muka gada tun lokacin kaka da kakanin.

“Abin da ya sa na tabbatar da haka shi ne, na yi yawo a wannan duniya daidai bakin gwargwado ta dalilin aiki ko na neman ilimi. Abin da ya fi ba ni shi sha’awa da mamaki na al’adar Hausawa shi ne, sai da na girma na gane matar mahaifina da ke tare da mahaifiyata ba ita ce ta haife ni ba, saboda ita ce take yi min komai, domin a gurinta nake.

“Haka shi ma dan’uwana ya samu kansa, ba za ka taba samun wannan dabi’a mai kyau ba in ba a cikin Hausawa ba. Bahaushe ya yi sa’a da ya kamata ya rike al’adarsa da alfaharin a fadin duniya, kuma har yanzu ba mu san abin da ake cewa mace ta yi yaji a gidanmu ba.”

A bana dai bikin rana rya fi mayar da hankali ne a kan yadda za a tabbatar da zaman lafiya da kaunar juna a tsakanin al’umma.

Ranar Hausa
Mustapha Ibrahim
+ postsBio
  • Mustapha Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/mustapha-ibrahim/
    Ma’aikatar REMASAB Ta Ƙaddamar Da Shirin Aikin Mai Da Shara Taki A Kano
  • Mustapha Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/mustapha-ibrahim/
    Cire Alamar PDP A Zaben Jihohi Biyu Ta Sa Sardauna Ya Nemo Wa Mabiyansa Mafita —Farfesa Sule Yau
  • Mustapha Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/mustapha-ibrahim/
    An Ƙirƙiro Da Shirin ‘Kano First’ Ne Don Sanya Wa Kanawa Kishin Jiharsu —Bala Gwagwarwa
  • Mustapha Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/mustapha-ibrahim/
    Idan Gwamna Abba Ya Ziyarci Kwalejin Bebeji Matsalarmu Za Ta Zo Ƙarshe – HOD Habib

MASU ALAKA

Ranar Hausa
Rahotonni

Ko Yakin Iran Zai Kawo Karshen Kawancen Amurka Da Kasashen Larabawa?

May 17, 2026
Ranar Hausa
Rahotonni

Yadda Sauya Shekar ‘Yan Siyasa Ta Sauya Fasalin Majalisar Dokokin Kasa

May 16, 2026
Abincin Da Ya Kamata Ku Ci Lokacin Al’ada
Rahotonni

Almajiranci:Matsala Ko Maslaha

May 10, 2026
Next Post
Abin Da Ya Sa Mata Suka Fi Fuskantar Yiwuwar Kashe Kansu —Farfesa Aishatu

Abin Da Ya Sa Mata Suka Fi Fuskantar Yiwuwar Kashe Kansu —Farfesa Aishatu

LABARAI MASU NASABA

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

June 4, 2026
Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

June 3, 2026
Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026
Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

June 3, 2026
Majalisa Ta Nemi Tinubu Ya Canza Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci Don Kawo Ƙarshen Kashe-kashe

’Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice Daga APC Zuwa ADC da PRP

June 3, 2026
An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

June 3, 2026
Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

June 3, 2026
Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

June 3, 2026
Za A Fara Buga Gasar Kofin Sarkin Gombe Bayan Masu Ruwa Da Tsaki Sun Cimma Matsaya

Za A Fara Buga Gasar Kofin Sarkin Gombe Bayan Masu Ruwa Da Tsaki Sun Cimma Matsaya

June 3, 2026
Hada Kai Da ’Yan Awaren Yankin Taiwan Ba Zai Haifar Da Ɗa Mai Ido Ba

Hada Kai Da ’Yan Awaren Yankin Taiwan Ba Zai Haifar Da Ɗa Mai Ido Ba

June 3, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.