Gwamnatin Jihar Kano za ta horar da jarumai 100 na masana’antar Kannywood kan harkar fim da kasuwanci kamar yadda shugaban hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano Abba El Mustapha ya bayyana wa ‘yan jarida.
Alhaji Abba El-mustapha ya jaddada akkawuran gwamnatin Engr. Abba Kabir Yusuf inda ya ce zai wadata masana’antar fina-finan kannywood da dabarun zamani wajen shirya fina-finai.
- Ambaliya: Uwargidan Gwamnan Yobe Ta Janjanta Wa Al’ummar Maiduguri
- Me Ya Haddasa Cacar Baki Tsakanin Kwankwaso Da PDP?
Abba El-Mustapha ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da fom 100 na aikace-aikace ga ’yan masana’antar Kannywood na shirin horarwa na tsawon watanni biyu kan harkar fim da kasuwanci, wanda Cibiyar Fina-Finai ta Jihar Kano za ta gudanar.
Abba El-mustapha ya bayyana cewa shirin wani bangare ne na kokarin da gwamnatin Jihar Kano ke yi na bunkasa fasahar ‘yan masana’antar Kannywood, da samar musu da dabarun shirya fina-finai na zamani, da ka’idojin da’a, da dabarun kasuwanci don bunkasa dogaro da kai.
Ya ci gaba da cewa shirin na da nufin baiwa mahalarta taron ilimi da kayan aikin da suka dace don samun nasara a harkar fim a lokuta masu zuwa,ya kuma bukaci daukacin mahalarta taron da su yi amfani da wannan dama mai kima da gwamnatin jihar Kano ta ba su, tare da jaddada muhimmancin yin fim din.
Horar da su don ciyar da sana’o’insu gaba da kuma ba da gudummawa ga ci gaban masana’antar fim ta cikin gida.
Manufar wannan horon ita ce fadakar da masu shirya fina-finai namu da ayyukan zamani da ka’idojin da’a, ta yadda za su kasance masu dogaro da kai da samun nasara a harkokinsu,” in ji Abba El-mustapha.
A karshe ya yaba da gagarumin goyon baya da hadin kai daga gwamnati wajen aiwatar da shirin da sauran tsare-tsare da ke amfanar masana’antu.
A nasa jawabin shugaban kungiyar masu harkar fim ta Jihar Kano, Malam Alhassan Kwalle, ya bayyana matukar godiya ga gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa jajircewarsa na inganta masana’antar a jihar.
Ya ce muna godiya ga Gwamna Yusuf da ya dauke mu a matsayin wadanda suka cancanta,da kuma wannan damar don inganta kwarewarmu kuma daga karshe ina kyautata zaton da wannan horo da zamu samu,muna da tabbacin cewa mambobinmu za su iya yin gogayya da takwarorinsu na duniya.