Kwamishinan ma’aikatar noma da kula da albarkatun kasa na jihar Kano Dakta Yusuf Jibrin Rurum, ya bayyana cewa, gwanamatin jihar ta mayar da hankali domin tabbatar an habaka noman zobo.
Dakta Yusuf ya ci gaba da cewa, har ila yau gwamnatin jihar na kokari wajen ganin ana fitar da ganyen zobon da ake noma wa a jihar zuwa kasashen waje, musamman domin a kara samawar da jihar da kudin musaya na ketare.
- Nijeriya Ta Yi Haramar Tarbar 2023 Da Harkokin Babban Zabe
- Sharhi:Al’ummar Kasar Sin Na Sa Ran Rungumar Sabuwar Rayuwa Cikin Sabuwar Shekara
Kwamishinan ya bayyana hakan ne a jawabinsa yayin wata ziyarar aiki da ya kai Cibiyar noma ta Afirka da ke jihar Kano.
A cewar Kwamishinan, jihar kano na cikin murna bisa samun masu zuba jarinsu a fannin na noman ganyen sabo a jihar.
Dakta Yusuf ya kara da cewa, gwamnatin kano za ta taimaka wajen ganin an kara fadada noman zobo, musamman domin a samu nasara.
A cewar Dakta Yusuf, mun gane wa idanuwanmu yadda ake yin amfani da fasahar zamani wajen sarrafa na zobo zuwa sauran kayan sha.
Kwamishinan ya kara da cewa, wannna shi ne, abin da muke son mu gani masu noman na zobo na yi a jihar, mussamna domin kara fadada sana’ar ta nomansa a jihar.
A nasa jawabin tun da farko, babban jami’ia kamfanin sarrafa abinci na Mumin Foods, Alhaji Abdullahi Usman ya bayyana cewa, kamfanin ya faro ayyukansa ne tun a shekarar 2019.
Alhaji Abdullahi ya ce, kamfanin ya dade yana fitar da zobon da aka noma wa a kasar nan zuwa wasu kasashen duniya.