Gwamnatin Jihar Kano, ta bayyana shirinta na sake buɗe makarantun kwana guda 10 da gwamnatin baya ta rufe, domin ƙara bai wa yara mata damar samun ilimi, musamman waɗanda ke yankunan karkara.
Mai kula da ilimin ’ya’ya mata a ma’aikatar ilimi ta Jihar Kano, Hajiya Amina Kassim, ce ta bayyana hakan yayin da ta ke amsa tambayoyi daga manema labarai a wani taron tattaunawa da aka shirya kan kasafin kuɗi game da ilimin yara mata.
Taron ya samu tallafi daga Malala Fund kuma Bridge Connect Africa Initiative (BCAI) ce ta shirya.
Hajiya Amina, ta bayyana cewa al’ada da matsin tattalin arziƙi suna daga cikin dalilan da ke hana ’yan mata samun damar zuwa makaranta a jihar.
Sannan ta ce nisan makarantun na ɗaya daga cikin manyan matsalolin da ke hana yara, musamman mata, ci gaba da karatu bayan kammala firamare.
Ta bayyana cewa gwamnatin jihar ta bayyana ayyana dokar ta-ɓaci a harkar ilimi, kuma ta kashe biliyoyin Naira wajen gyara da sabunta makarantun kwana, inda ta ce “nan ba da jimawa ba za a sake buɗe su don yara mata su ci gaba da samun ilimi.”
Ta kuma ƙara da cewa wasu daga cikin makarantun da ke aiki kamar WTC Kano da GGS Dala na karɓar yara daga yankunan da ke kewaye da su, kuma za a yi amfani da irin wannan tsari a sauran makarantun da za a sake buɗewa.
Hajiya Amina ta ƙara da cewa ofishinta ya samu amincewa daga ma’aikatar don gudanar da bincike a wasu yankuna da ke fama da yawan yara mata da ba sa zuwa makaranta ko kuma waɗanda suka daina karatu, don gano matsalolinsu da kawo mafita.
A nasa ɓangaren, Abdulaziz Musa, wanda shi ne mai kula da shirin “Bridging Access to Girls Education” na BCAI, ya bayyana cewa manufar taron ita ce tattauna ci gaba da ƙalubale da kuma amfani da kuɗaɗen da aka ware don ilimin ’yan mata tare da wakilan gwamnati, ƙungiyoyin fararen hula, da kuma ’yan jarida.
Ya ce duk da ci gaban da aka samu, har yanzu akwai ƙalubale mai yawa, don haka akwai buƙatar haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da ƙungiyoyi masu zaman kansu domin ciyar da harkar gaba.
Ya ƙara da cewa sun samar da wani tsarin kasafin kuɗi da ya dace da buƙatun mata wanda gwamnati za ta iya amfani da shi wajen tsara yadda za a kashe kuɗin da aka ware don inganta ilimin yara mata a Jihar Kano.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp