Gwamnatin Jihar Katsina ta fara bayar da magani kyauta ga waɗanda ke fama da zazzaɓin cutar taifod a jihar.
Wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na hana yaɗuwar cutar da kuma rage wahalar da mutane ke sha wajen neman magani.
- NiMet Ta Yi Hasashen Samun Mamakon Ruwan Sama A Sassan Nijeriya Cikin Kwana 3
- Gwamnonin Nijeriya Sun Yi Ta’aziyyar Waɗanda Suka Rasu A Ambaliyar Ruwa A Adamawa
Kwamishinan YaÉ—a Labarai na jihar, Bala Salisu Zango, ya ce gwamnati ta ware asibitoci biyar domin gudanar da wannan shiri.
WaÉ—annan asibitoci su ne:
1. Asibitin Gwamnati na Katsina
2. Asibitin Turai Yar’Adua
3. Asibitin Amadi Rimi
4. Asibitin Jibia
5. Asibitin Funtua
Zango, ya ce gwamnati na ƙoƙarin tabbatar da cewa duk wanda ke fama da cutar ya samu magani cikin sauƙi ba tare da biyan kuɗi ba.
Zazzabin taifod yana yaÉ—uwa ne musamman a lokacin damina, kuma yana da nasaba da amfani da ruwa mai datti da rashin tsafta.
Alamomin cutar sun haÉ—a da ciwon ciki, ciwon kai, da gajiyar jiki.
Gwamnati ta shawarci jama’a da su riƙa kula da tsafta da kuma hanzarta zuwa asibiti idan sun ga irin waɗannan alamomi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp