Gwamnatin Jihar Katsina ta bayar da umarnin rufe makarantu 32 na gaba da sakandare masu zaman kansu da ke aiki ba tare da lasisi ko sahalewar hukumomin da ke kula da ilimi ba a jihar.
Kwamishinan Ilimi na Manyan Makarantu, Fasaha da Sana’o’i, Dr. Muhammad Isah Kankara, ne ya bayyana hakan yayin kare kasafin kuɗin ma’aikatarsa na shekarar 2026 a gaban kwamiti ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan tsare-tsare da tattalin arziƙi, Malik Anas, a Katsina.
- Ina Aka Kwana Batun Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Dazukan Jihar Katsina?
- Katsina Za Ta Ɗauki Nauyin Karatun Mahaddata Alƙur’ani – Gwamna Radda
Dr. Kankara ya ce binciken ma’aikatar ya gano cewa da dama daga cikin makarantun masu zaman kansu suna gudanar da aiki ne ba bisa ƙa’ida ba, ba tare da cika ƙa’idojin ƙasa ba.
Ya bayyana cewa wannan mataki ya zama dole domin kare ɗalibai da tabbatar da ingancin ilimi a fadin jihar.
“Bincikenmu ya nuna cewa wasu makarantun masu zaman kansu suna aiki ne ba tare da amincewar hukumomin da suka dace ba,” in ji shi.
Kwamishinan ya amince cewa rufe makarantun ya shafi kuɗaɗen shiga na cikin gida (IGR) da ake sa ran samu a shekarar 2026, domin da yawa daga cikin makarantun da aka rufe suna taka muhimmiyar rawa wajen samar da kuɗaɗen shiga ga ma’aikatar.
“Adadin kuɗaɗen shiga zai ragu a bana saboda yawancin waɗannan makarantun da aka dakatar suna cikin waɗanda ke taimaka mana wajen samar da kuɗi. Za mu iya dawo da su ne kawai idan suka cika sharuddan da doka ta tanada,” in ji Kankara.
A yayin zaman, shugaban kwamitin kasafin kuɗi, Malik Anas, ya umarci ma’aikatar da ta gabatar da cikakken jerin makarantun da ke da lasisi da waɗanda ba su da shi, tare da hasashen kudaden shiga daga kowacce.
Dr. Kankara ya bayyana cewa ma’aikatar tana tattara bayanan da ake buƙata kuma za ta mika cikakken rahoto nan ba da jimawa ba.
Ya ƙara da cewa makarantu guda bakwai (7) kawai daga cikin 39 masu zaman kansu ne aka tabbatar da sahihancinsu kuma suna ci gaba da aiki bayan wannan rufe-rufe.
Kwamitin ya yaba wa ma’aikatar bisa tsaurara dokoki don tabbatar da bin ƙa’idoji, tare da umartar ta da ta kawo sabbin bayanai kafin kasafin shekara mai zuwa.