Gwamnatin Jihar Katsina ta ce za ta binciki kisan mutane 41 da ‘yan ta’adda suka yi a dajin Yargoje da ke karamar hukumar Kankara a jihar.
Alhaji Ahmed Ibrahim-Katsina, mai bai wa gwamna Aminu Masari shawara kan harkokin tsaro ne, ya bayyana hakan a ranar Asabar a Katsina.
- An Gabatar Da Shirin Tallata Bikin Fitilu Na Gargajiyar Sin A Afrika Ta Kudu Da Habasha
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Alkali A Kotu A Jihar Imo
A cewarsa, lamarin da ya yi sanadin jikkatar mutane biyu ya shafi kowa ciki har da Gwamna Masari.
“Gwamnan ya yi bakin ciki matuka, kuma ya ba da umarnin a karfafa tsaro cikin gaggawa a yankin.
“Ya kuma ba da umarnin a kafa kwamitin bincike kan lamarin.
“Muna so mu yi cikakken binciken don gano yadda lamarin ya faru,” in ji shi.
Ya kara da cewa Masari ya kuma bayar da umarnin a kai kayan agaji cikin gaggawa ga iyalan wadanda abin ya shafa.
“Gwamnati ta kai dauki yankin kuma muna so mu tabbatar wa mazauna jihar cewa gwamnati ta ba da fifiko kan tsaro.
“Daga dabarun da muke bi, mun yi imanin cewa wannan lamarin zai tarihi.”
Ya ce binciken farko ya nuna cewa mutane 41 ne suka mutu a harin kwantan bauna.
“Sakamakon kwamitin binciken zai taimaka mana wajen daukar matakai wajen hana afkuwar irin wannan mummunan lamari nan gaba,” in ji Ibrahim-Katsina.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), ya ruwaito cewar harin ya auku ne a ranar Alhamis.