Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayyana Asabar din kowane jarshe wata a matsayin ranar tsaftar muhalli a jihar.
Gwamnan, ya bayyana haka ne wajen kaddamar da shirin tsaftar muhalli ta kowace karshe wata a jihar.
- Masu Baje Kolin Kaya Kimanin 300 Za Su Halarci Bikin Kasuwancin Yammacin Afirka A Legas
- Gwamnatin Tarayya, Bankin Duniya Da Cibiyar IITA Za Su Bunkasa Noma Ta Fasahar Zamani
Gwamnan wanda mataimakinsa, Sanata Umar Abubakar Tafida ya wakilta, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yanke shawarar sake bullo da kuma karfafa shirin tsaftacce muhalli na wata ne saboda muhimmancinsa ga lafiyar jama’ar.
“Tsaftar muhalli da ruwan sha na da matukar muhimmanci ga jin dadin jama’a don rage cututtukan iska da na ruwa,” in ji shi.
Ya kara da cewa, “Gwamnatina za ta ci gaba da kula da harkokin kiwon lafiya a Jihar Kebbi, a koda yaushe domin tabbatar da cewa al’ummarmu sun kasance ‘yan jiha masu koshin lafiya kuma masu amfani cikin al’umma”.
Gwamnan ya ja kunnen jama’a da kada su rika sanya kansu cikin hatsari ta hanyar kazantar muhalli don gujewa cututtuka.
Da yake jawabinsa tun daga farko, Kwamishinan Ma’aikatar Tsaftar Muhalli, Alhaji Musa Muhammad Tungulawa, ya ce gwamnan ya umarci ma’aikatar da ta ci gaba da gudanar da gangamin tsaftace muhalli da wayar da kan jama’a don samun nasara.
“A ranar Asabar din karshe na kowane wata, za a gudanar da atisayen ne a babban birnin jihar, Birnin Kebbi, da kuma dukkan kananan hukumomin 21 na jihar,” in ji shi.
Kwamishinan ya bayyana cewa gwamna Nasir Idris ya ba da fifiko kan harkokin muhalli da kuma samun cikakkiyar tsafta a tsakanin ‘yan jihar.
Sarkin Gwandu, Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar, ya yaba wa gwamnan jihar kan matakin da ya dauka na tabbatar da tsaftar muhalli a jihar.
Sarkin ya umarci jama’a da su kasance masu biyayya da addu’a domin samun nasarar gwamnatin.
“Yin biyayya ga shugabanni yana da su yi aiki, yayin da shugabanci nagari ke ba jama’a kuzari don samun ingantacciyar rayuwa, wasu jihohi da masarautu a wasu wurare suna cikin mawuyacin hali, jihar Kebbi tana cikin kwanciyar hankali da tsaro mai kyau mu ci gaba da zaman lafiya da juna”, in ji Sarkin Gwandu.