Gwamnatin Jihar Kebbi ta zargi Sanatoci biyu masu ci daga jihar, Adamu Aliero da kuma Sanata Dokta Yahaya Abdullahi da yi wa Majalisar Dattijai bayanai na hana bukatar da gwamnatin jihar ta yi na maida wa jihar kudaden da ta yi ayyukan wasu titunan tarayya guda biyu a kan kudi Naira Biliyan shida da Naira Miliyan dari bakwai da gwamnatocin baya suka gina a jihar.
Kwamishinan ma’aikatar ayyuka da sufuri na jihar, Alhaji Abubakar Chika Ladan ne ya bayyana kan a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai kan a Birnin Kebbi, ya ce “An tafka kura-kurai da karya da ke tattare da ikirarin gwamnatin jihar na mayar da kudaden a hanyoyin tarayya, kuma sanatocin biyu sun mayar da shi tamkar wata kasuwa, in ji shi”.
- Wata Mata Ta Shiga Hannu Kan Zargin Kashe Kishiyarta Da Tabarya A Bauchi
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 4 Sun Kwato Alburusai A Kaduna
Ya ce babu lokacin da gwamna ko wani jami’in gwamnatin jihar suka yi ikirarin gina hanyoyin biyu ba, “Duk abin da muka yi shi ne bin hakkin jihar na biyan diyya da abin da ya dace a jihar Kebbi kamar yadda aka yi wa wasu jihohi.
“Ba mu san ko wace shaida Sanata Adamu Aliero da Sanata Yahaya Abdullahi suke nema kan batun biyan jihar, shi ne ya bayar da kwangilar daya daga cikin hanyoyin biyu a lokacin da yake gwamna, shi ma ya fadi haka a zaman majalisar dattawa to mene ne hujjar shi na cewa sai mu gabatar da hujjoji aikin da muka yi. Duk takardun hujjojin da ake so suna a gaban Majalisar Dattawa da na wakilai, wacce hujja ake nema kuma”, in ji kwamishinan Abubakar Chika ladan.
Ya kara da cewa tun bayan umarnin da majalisar dattijai ta bayar na cewa jami’an gwamnatin jihar Kebbi su bayyana a gaban kwamitinta mai kula da lamuni da basussuka tare da duk wasu takardu da suka dace, domin kare ikirarin sake biya na gina titunan gwamnatin tarayya guda biyu a jihar.
Ya ce bisa ga bayanin, an gina titin tarayya guda biyu, hanya Dabai-Mahuta-Koko mai tsawon kilomita 91 a tsakanin shekarar 2006-2011 a kan kudi N5,070,912,911.47 da gwamnatin Adamu Aliero ta yi, amma gwamnatin Saidu Dakingari ta kammala shi a shekarar 2011.
Haka kuma Malando-Garin, Saidu Dakingari ne ya gina titin Baka -Ngaski-Warra mai tsawon kilomita 42 daga shekarar 2008-2013 tare da gadar mai fadin mita 90 mai tsawon mita 6 akan kudi N2,200,918,185.78.
“Lokacin da wannan gwamnati ta zo a shekarar 2015, ta gano cewa gwamnatin tarayya na mayarwa gwamnatocin jihohin kudaden da jihohin suka gina a yankinsu.
“A shekarar 2016 gwamnatin jihar ta umurci kwamishinan ayyuka na lokacin, Alhaji Atiku Bunu da ya tuntubi ma’aikatar ayyuka ta tarayya da bukaci cewa gwamnatin Abubakar Atiku Bagudu na da son a mayar da kudaden hanyoyin guda biyu da kuma wasu guda uku da suka kai Naira Biliyan 10.08.
“Sai dai ma’aikatar ayyuka ta tarayya za ta iya amincewa da hanyoyin biyu da wanda Aliero da Dakingari suka yi domin mayar da su, domin an yi su ne kafin shekarar 2015 lokacin da gwamnatin tarayya ta ba da umarnin dakatar da gina titunan gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi suka yi, an ba da izinin ne a shekarar 2020.
“Bayan haka ma’aikatar ta ba da yanke shawarar mayar da kudaden gina hanyoyin biyu zuwa Naira biliyan 6.7 kuma an ba da izinin a ranar 7 ga Satumba, 2022,” in ji shi.
Ya ce a rubuce ne jihar ta mutunta gayyatar da majalisar dokokin kasar ta yi mata domin kare ikirarinta. Ya kara da cewa, bisa wasikar da majalisun dokokin kasar biyu suka rubuta wa gwamnatin jihar, an mika dukkan takardun da suka shafi aikin gina hanyoyin zuwa ga majalisar dattawa da ta wakilai a ranar 27 ga Satumba, 2022.
“A ranar 6 ga watan Oktoba, 2022 ne majalisar dokokin kasar ta gayyaci jihar da ta bayyana gaban kwamitocin majalisun biyu, na jagoranci kwamitin mutum hudu zuwa majalisar dattawa da ta wakilai, mun samu nasarar gabatar da kararmu a gaban kwamitin majalisar wanda daga baya ya jagoranci kwamitin. Don amincewa da biyan bashin da majalisar ta yi amma majalisar dattawa ta bukaci mu jira wasu umarni amma ba mu ji su ba har muka dawo Jihar.”
Kwamishinan ya ce majalisar dattijai ta sake ba wa jami’an jihar damar bayyana a gabanta a ranar 30 ga watan Nuwamba, 2022, “Ya kamata a lura da cewa duk takardunmu da suka dace suna hannun kwamitin majalisar,” inji shi.
Daga karshe ya ba da tabbacin bayyana a gaban kwamitin majalisar dattijai don kare abin da kudaden da suke neman gwamnatin tarayya ta biya Jihar Kebbi.