Gwamnatin Jihar Kebbi ta nuna shirinta na hada gwiwa da masanan kasar Masar wajen bunkasa noma da kiwo.
Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin kwararrun masana ‘yan kasar Masar da suka ziyarce shi a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi.
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Daina Ciyar Da Fursunoni Abinci
- ‘Yansanda Sun Kama Mutumin Da Ya Kashe Matarsa A Adamawa
Bagudu ya shaida wa maziyartan nasa cewa, gwamnatin ta shirya tsaf don hadin gwiwa da hadin kai a matsayin muhimman abubuwan ci gaba, inda ya ce jihar Kebbi ta samu tagomashi wajen noma sosai, kuma an bayyana jihar a matsayin jihar ta biyu mafi yawan kiwon dabbobi a kasar nan.
Hakazalika, jihar ta zama hanyar shigar kasashen Afirka ta yamma wajen kiwon dabbobi saboda kyakkyawan wurin da take da iyaka da Jamhuriyar Nijar da Jamhuriyar Benin.
Ya kara da cewa, jihar Kebbi ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta bangarori uku da Kwanni a Jamhuriyar Nijar da kuma Maleville a Jamhuriyar Benin kan bunkasa kiwon dabbobi, noma da cinikayya
Gwamnan ya bayyana al’ummar jihar Kebbi a matsayin masu aiki tukuru kuma a shirye suke su tsara hanyoyin zamani wajen noma da kiwo.
Sanata Bagudu ya yaba wa shugaban kungiyar manoma shinkafa ta kasa RIFAN, Alhaji Aminu Goroyo bisa yadda ya kai ziyarar kwararu masanan kasar Masar a jihar da kuma shirye-shiryen hadin gwiwa kan fannin noma.
Gwamnan ya bayyana karara cewa zababben shugaban kasar Nijeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi alkawarin dorawa kan nasarorin da aka samu kan farfado da aikin gona don samar da abinci da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar a matakin kasa.
Shugaban RIFAN na kasa Alhaji Aminu Goronyo tun da farko ya shaida wa gwamnan cewa kwararrun masanan kasar Masar karkashin jagorancin Janar Walid Yahia Soliman Morsy sun shigo jihar Kebbi ne domin hadin gwiwa kan harkokin noma da Kiwon dabbobi.
Goronyo ya nuna cewa kwararrun za su bunkasa kusan kilomita dari tara na filin Fadama a jihar ta hanyar horas da manoma da aiwatar da tsarin noman zamani da fasaha da kuma kwarewa.
Daga nan ya yaba wa Gwamna Atiku Bagudu a matsayinsa na mataimakin shugaban hukumar kula da samar da abinci ta kasa kan bunkasa noma ta yadda kananan manoma da sauran manoma za su samu kudi da noma wanda hakan ya haifar da karuwar amfanin gona da bunkasa tattalin arziki.