Baraka tsakanin gwamnatin Jihar Kogi da kamfanin simintin Dangote na dada zafafa sakamakon umarnin da gwamna Yahya Bello ya bayar na rufe kamfanin cikin sa’oi 48.
Leadership Hausa ta rawaito cewar gwamnatin Kogi ta hannun kwamishinan yada labaranta, Kingsley Fanwo, ta bayyana cewar gwamna Bello ya bukaci kamfanin Dangote da ya mutunta matsayin da Majallisar Dokokin jihar ta dauka na ba da umarnin rufe kamfanin har zuwa lokacin da Dangote zai gabatar mata da bayanan da ta nema daga hannunsa dangane da mallakar kamfanin siminiti Obajana da filayen da ke wurin.
- A Watan Nuwamba Za Mu Raba Sabbin Katunan Zaben Da Aka Yi Rijista —INEC
- Kwastam Ta Kama Haramtattun Kayayyaki Na Sama Da Naira Miliyan 200 A Bauchi
Wannan na zuwa ne bayan gaza bayyana da da Dangote ya yi gaban gwamnatin jihar, bayan aike masa da sammaci da ta yi.
Bello ya ce a matsayinsu na hukuma za su kare matakan da gwamnati ke dauka daga kama karya, yayin da ya jaddada wa jama’ar jihar aniyarsa ta kare muradunsu ba tare da saba ka’ida ba.
Sanarwar kwamishinan ta ce ganin yadda gwamnan ke da goyon bayan mutanen jihar Kogi sama sa miliyan hudu , zai ci gaba da daukar duk matakan da suka dace wajen kare muradunsu ta hanyar tanade-tanaden dimokuradiyya.
Kwamishinan ya bukaci jama’ar jihar da su kauce wa daukar doka a hannu domin bai wa hukumomi damar daukan matakan da suka dace.
A karshe gwamnan ya bada umarnin sakin manyan motocin Dangote da aka kama a sassan jihar sakamakon takaddamar da ake yi, yayin da ya bukaci jama’ar jihar da su tabbatar da ganin jihar ta dore a matsayin mai karbar bakin da ke bukatar zuba jari kamar yadda aka gani a shekaru bakwai da suka gabata.