Gwamnatin jihar Kogi ta tabbatar da aniyarta ta magance matsalolin ambaliya da zaizayar ƙasa ta hanyar aiwatar da muhimman ayyukan gine-gine da aka tsara domin samar da mafita ga matsalolin muhalli a faɗin jihar.
Kwamishinan yaɗa labarai da sadarwa na jihar, Kingsley Femi Fanwo, ya bayyana cewa gwamnatin Gwamna Usman Ododo ta ƙuduri aniyar inganta rayuwar al’umma ta hanyar gina muhimman abubuwan more rayuwa da za su tabbatar da tsaro, da ɗorewa da ingantacciyar rayuwa.
- Hakimin Da Aka Sace A Jihar Kogi Ya Shaki Iskar ‘Yanci
- Sojoji Sun Ceto Shugaban Fulani, Mutane 5 Daga Hannun Ƴan Bindiga A Kogi
Ya bayyana cewa sabbin magudanan ruwa da aka kammala a wurare irin su Etahi, da Omigbo da Olubojo a ƙaramar hukumar Ankpa sun fara aiki yadda aka tsara, inda ruwan sama ke taruwa cikin sauƙi kuma ana karkatar da shi, wanda hakan ke rage barazanar ambaliya.
Fanwo ya ƙara da cewa gwamnatin jihar na amfani da shirin Agro-Climatic Resilience in Semi-Arid Landscapes (ACReSAL) domin ƙarfafa matakan kare ambaliya da kuma dawo da filayen da ambaliyar da zaizayar ƙasa suka lalata. Ya ce wannan shiri ya zama ginshiƙi wajen samar da tsare-tsare mai ɗorewa a fannin muhalli.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp