Gwamnatin Jihar Kogi ta nuna matuƙar godiya ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa naɗin Farfesa Joash Ojo Amupitan, SAN, ɗan asalin jihar, a matsayin sabon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Kingsley Femi Fanwo, ya fitar ranar Alhamis, ya ce wannan naɗi ya nuna irin jajircewar Shugaba Tinubu wajen fifita ƙwarewa, cancanta, da haɗin kan ƙasa wajen zaɓen shugabanni hukumomin gwamnati.
- Tsaro: Gwamnan Kogi Ya Ayyana Yaƙi Da Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ka’ida Ba Da ‘Yan Bindiga
- Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Karyata Batun Yi Wa Kiristoci Kisan Ƙare Dangi
Fanwo ya bayyana Farfesa Amupitan a matsayin ƙwararren masani a fannin shari’a, wanda ya cancanci wannan matsayi saboda ƙwarewarsa, da gaskiyarsa, da adalcinsa, waɗanda suke da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da ingantaccen tsarin zaɓe a Nijeriya.
Ya ƙara da cewa gwamnatin Kogi da mutanen jihar suna tabbatarwa Shugaban Ƙasa da ƴan ƙasa cewa Farfesa Amupitan zai ci gaba da zama abin alfahari ga jihar da ƙasa baki ɗaya, ta hanyar gudanar da zaɓe mai gaskiya da sahihanci.
Fanwo ya taya sabon shugaban INEC murna bisa wannan babban aiki, yana masa fatan nasara, da samun hikima da basira wajen cika wannan muhimmin aiki ga Nijeriya.