Gwamnatin Jihar Neja ta umarci ‘yansanda da sauran jami’an tsaro a jihar da su kama mutanen da suka ka ki karbar tsofaffin kudi.
Sakataren gwamnatin Jihar Neja, Alh. Ahmed Ibrahim Matane, ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a Minna a ranar Litinin.
- Gwamnatina Za Ta Tabbatar An Fara Hako Mai A Bauchi Da Gombe – Tinubu
- Burundi Ta Jinjinawa Kwararrun Sin Bisa Tallafin Su A Fannin Raya Aikin Gona
Ya bayyana cewa har yanzu tsofaffin takardun Naira na nan daram kuma duk wanda aka kama ya ki karbarsu domin yin kasuwanci to zai fuskanci fushin doka.
A cewarsa, “Tsoffin takardun Naira na nan daram kuma duk wanda aka kama ya ki karba yana jawo wa ‘yan kasa wahala za a kama shi kuma a gurfanar da shi a gaban kuliya.”
Daga nan sai Matane ya bukaci al’ummar jihar da su gudanar da harkokinsu na yau da kullum sannan su kai rahoton duk mutumin da ya ki karban kudin tsofaffin kudin ga jami’an tsaro a jihar domin daukar matakin da ya dace.
Rashin samun sabbin takardun kudin da aka canja ya janyo wa jama’a kunci, ganin yadda ‘yan kasuwa suka ki karbar tsofaffin takardun naira, tare da dagewa a kan sabbi a matsayin hanyar musayar kudi.
Wasu mazauna yankin da suka zanta da wakilinmu, sun koka da irin wahalhalun da tsarin ya haifar, inda suka yi kira ga gwamnatin jihar da ta tashi tsaye domin rage radadin da jama’a ke ciki.
Wannan dai na zuwa ne bayan wa’adi na biyu da CBN da Gwamnatin Tarayya suka ware na ranar 10 ga watan Fabrairu, 2023 na daina amfani da tsofaffin kudin.
Amma wata kotun koli ta dakatar da su kan cikar wa’adin da suka ware na daina amfani da tsofaffin takardun kudin.