Gwamnatin Jihar Neja ta sanar da cewa jami’an tsaro sun kama Abubakar Abba, shugaban ƙungiyar ta’addanci ta Mahmuda kuma ɗaya daga cikin mafi hatsari a Yammacin Afirka.
A cewar sanarwar da Babban Sakataran Yaɗa Labarai na Gwamna Mohammed Bago, Bologi Ibrahim, ya fitar, an kama Abba a yankin Wawa, da ke ƙaramar hukumar Borgu, kuma an kai shi Abuja domin ci gaba da bincike.
- ADC Ta Dakatar Da Shugabanta Da Wasu Jiga-jigai 3 A Kebbi
- Tambuwal: ’Yan Nijeriya Sun Soki EFCC Kan Rashin Kama Okowa, Ganduje Da Yahaya Bello
Gwamna Bago ya ce wannan nasara tana nuna jajircewar Shugaba Bola Tinubu wajen kare rayukan ’yan Nijeriya.
“Gaskiya ne jami’an DSS sun kama shugaban ƙungiyar ta’addanci ta Mahmuda, Abubakar Abba, sun kama shi a raye ta hanyar dabarun leƙen asiri.
“Wannan babbar nasara ce a gare mu a Jihar nan da kuma ƙasar gaba ɗaya. Shugaba Tinubu ya cancanci yabo kan wannan labari mai daɗi,” in ji gwamnan.
Ya ƙara da cewa gwamnati ta ƙudiri niyyar kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro da kuma inganta rayuwar ’yan Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp