Gwamnatin Tarayya ta kirkiro Cibiyar Nazarin Al’adu ta Nijeriya (NACUS), wata cibiya ce ta musamman da za ta horar da daidaikun mutane don yin sababbin abubuwa da kuma bunkasa al’adu da tarihin Nijeriya.
Otunba Biodun Ajiboye, Babban Sakatare na Cibiyar Wayar da Kan Al’adu ta Kasa (NICO) ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
- An Kira Taron Dandalin Tattaunawa Kan Musayar Al’adu Tsakanin Sin Da Faransa
- Bikin Al’adun Gargajiya Na Rigata Karo na 3 Zai Gudana A 8 Ga Fabrairu A Yauri
A cewar sakataren zartaswa, makarantar ta musamman za ta kasance babbar cibiyar horar da al’adu ta kasa.
Ya ce cibiyar wadda ta kasance makarantar horaswa ce ta NICO a yanzu ta samu amincewar hukumar kula da ilimin fasaha ta kasa (NBTE).
Ya kara da cewa NACUS ta samu takardar shedar gudanar da wani shiri da zai kai ga bayar da lambar yabo ta ‘National Diploma in Cultural Administration & Management (NDCAM)’, yayin da shirinta na Difloma na gaba zai yi hadin guiwa da alaka da Jami’ar Jihar Nasarawa.
A cewar Ajiboye, ci gaban da aka samu ya nuna cewa Nijeriya a karkashin wannan gwamnati ta ga bukatar rungumar al’adu a matakin koli.
Tuni aka fara kokarin shigar da ma’aikata na tarayya don ganin an karbi takardar shedar makarantar a ma’aikatan gwamnati da sauran su.