Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta bayar da umarnin rufe dukkan iyakokin kasar domin gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki da za a yi ranar Asabar.
Babban Kwanturola Janar na Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), Isah Jere Idris, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Alhamis, inda ya ce dokar hana zirga-zirga daga dukkan iyakokin kasa ta fara aiki ne daga karfe 12:00 na ranar Asabar, 25 ga Fabrairu. zuwa Lahadi, 26 ga Fabrairu, 2023.
- Shugaban NIS Ya Kaddamar Da Ofishin Fasfo Na Zamani A Zariya
- Sabon Kwanturolan NIS A Ribas Ya Gargadi Jami’ansa Kan Bin Dokokin Aiki A Zaben 2023
Ya ce, “Saboda zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da za a yi a ranar 25 ga Fabrairu, 2023, gwamnatin tarayya ta ba da umarnin rufe dukkan iyakokin Najeriya daga ranar Asabar 25 ga Fabrairu zuwa Lahadi 26 ga Fabrairu, 2023.
“An dauki wannan matakin ne don takaita zirga-zirga a kan iyakoki a lokutan zaben, don Jama’a su lura kuma su tabbatar da bin doka.”
Don haka, Idris Jere ya umurci daukaci Jami’an NIS na Jihohin da ke kan iyaka da su tabbatar da aiwatar da dokar.