Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi Allah wadai da harin da aka kai wa ‘yan sa-kai a dajin Yargoje da ke cikin Æ™aramar hukumar Kankara ta jihar Katsina.
BBC ta rawaito cewa, wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Æ™asar, Malam Garba Shehu, ya fitar ya ce harin wanda ‘yan bindiga suka kai ya yi sanadin mutuwar ‘yan sa- kan da dama.
- Tinubu Yana Kaunar Nijeriya, Ku Zabe Shi – Buhari Ga ‘Yan Nijeriya
- Gwamnonin APC Sun Gana Da Buhari Kan Bukatar Cire Wa’adin Karbar Tsofaffin Kudi
‘Yan bindigar sun yi wa ‘yan sa-kan kwanton É“auta a dajin a lokacin da suke Æ™oÆ™arin Æ™wato wasu shanu da aka sace.
Shugaban Æ™asar ya bayyana alhininsa kan rasuwar jami’an sa-kan tare da jajanta wa iyalansu, yana mai cewa Nijeriya ba za ta manta da sadaukarwar da suka yi na kare Æ™asa, tare da yaÆ™ar miyagun laifuka a Æ™asarsu ba.
“Muna addu’a tare da jajanta wa iyalan mamatan a wannan lokaci na alhini. Muna addu’ar Allah ya gafarta musu” in ji Buhari.
Jihar Katsina da sauran jihohin arewa maso yammacin Æ™asar na fama da matsalolin ayyukan ‘yan bindiga, waÉ—anda ke yawan kai hare-hare, tare da sace mutane domin neman kuÉ—in fansa.