Gwamna Ahmad Aliyu na Jihar Sakkwato ya kafa kwamitin mutane tara da za su yi binciki mukaman da tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya nada jim kadan kafin karewar wa’adin mulkinsa.
Kwamitin wanda ke karkashin jagorancin tsohon ministan ‘yan sanda, Maigari Dingyadi an dora masa aikin nazarin nadin sarakunan gargajiya da Tambuwal ya yi da manyan makarantu takwas da gwamnatinsa ta sauya wa suna.
- Ko Me Manufar Argentina Ta Fara Biyan Bashin Waje Da Kudin Sin Rmb Ke Nufi?
- Tsadar Kayan Miya: Mazauna Abuja Sun Koma Yin Miya Da Gauta
A sanarwar da kakakin gwamnan, Malam Abubakar Bawa ya sanya wa hannu a ranar Litinin, ta ce kwamitin zai duba batun canza wa wasu manyan makarantu mata wuri da nadin shugabannin zartawas makarantun da gwamnatin Tambuwal ta yi tare da bai wa gwamnati shawarar da ya kamata.
LEADERSHIP Hausa ta ruwaito cewar jim kadan da rantsar da shi, Gwamna Aliyu ya dakatar da dukkanin sarakunan gargajiya da Tambuwal ya nada tare da soke canza wa manyan makarantu suna.
Manyan makarantun da Tambuwal ya sauyavwa suna su ne; Jami’ar Jihar Sakkwato wadda aka mayar Jami’ar Abdullahi Fodiyo domin karrama fitaccen malamin da duniya ke amfana da iliminsa da Jami’ar Ilimi ta Sakkwato zuwa Jami’ar Ilimi ta Shehu Shagari da kwalejin ilimi wadda aka mayar Kwalejin Ilimi ta Ibrahim Dasuki a bisa ga karramawa ga Sarkin Musulmi na 18 sai sabon asibitin koyarwa wadda aka radawa sunan Sarkin Musulmi wato Asibitin Koyarwa na Sultan Sa’ad Abubakar da sauransu.