Gwamantin tarayya ta fara yunkuri ganin ta fargado da inganta sashin rarraba wutar lantarki a Nijeriya, inda za ta fara shirin da kamfanonin raba wutar lantarki guda biyu da ba sa kwazo.
A cikin wata sanarwar manema labarai da mai magana da yawun ministan wutar lantarki, Bolaji Tunji ya fitar, matakin ya biyo bayan nazarin kalubalen da suka yi katutu ga kamfanonin rabar da wutar lantarki a kasar nan ne, ciki har da gibin mulki, nakasu na ababen more rayuwa, da gazawar kasuwanci.
- Adadin Wuraren Cajin Ababen Hawa Masu Aiki Da Lantarki Na Sin Ya Karu Da 47.6% A Shekara
- Nijeriya Na Bukatar Dala Biliyan 10 Kowace Shekara Domin Samun Ingantacciyar Wutar Lantarki — Minista
Ministan wutar lantarki, Cif Adebayo Adelabu, ne ya bayyana shirin bayan wata ganawa da hukumar hadin kan kasa da kasa ta Japan (JICA), wadda ta gabatar da taswirar hanyoyin da za a bi a gyara da farfado da tsarin rabar da wuta a Nijeriya.
Shirin gyaran a matakin gwaji, zai fara ne a watan Mayu da Agustan 2025, kuma za a yi da kamfanin rabar da wuta guda a Arewa da wata guda a Kudu. Na da nufin nuna samfurin da za a iya maimaitawa don jujjuyawar aiki, hada sake fasalin cikin gida, da sa ido na tarayya don samun ci gaba cikin sauri a isar da wutar lantarki ga jama’a.
Ministan ya kara da cewa, “Ba za mu ci gaba da zura ido muna kallo kamfanonin raba wutar lantarki da ba su kokari suna nan ba tare da sauyi ba. Wannan gwajin ba wai zabi ne ga kamfanonin rabar da wutar lantarki da ba su kokari ba, a’a dole ne ma.”
A cewarsa, ba ga wannan akwai shirin kawo sauyi kan manyan kalubale da suka hada da lalata na’urorin wutar lantarki, gudanarwa, matsalolin yankuna da suke janyo cikas ga gudanar da ayyuka.
Ya umarci hukumar kula da wutar lantarki a Nijeriya (NERC) da ta tabbatar kamfanonin rabar da wutar lantarki sun bayar da hadin kan da ake bukata domin samun nasarar gudanar da aikin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp