Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya tare da haɗin gwuiwar hukumar wayar da kai ta ƙasa (NOA) sun ƙaddamar da kamfen ɗin wayar da kan jama’a kan laifukan da ake aikatawa a intanet (cybercrime) a faɗin ƙasar nan, inda suka buƙaci matasa su kasance masu lura da amfani da fasahar zamani cikin gaskiya da aminci.
An ƙaddamar da Cybercrime Awareness Walk na 2025 a birnin Abuja, inda matasa, da jami’an tsaro, da ƙungiyoyin farar hula suka halarta. Muhammad Abubakar Babadoko, ya ce wannan yunƙuri yana daga cikin dabarun gwamnati na ƙara ƙarfafa martani kan ƙaruwar laifukan yanar gizo a kasar.
- Hukumar Kwastam Ta Tara Naira Biliyan ₦658.6 A Watan Satumba — DG Na NOA
- AFCON 2023: Hukumar NOA Ta Tsunduma Gangamin Tara Wa Super Eagles Ɗimbin Magoya Baya – Minista
Babadoko ya ce yayin da bincike da gurfanarwa ke da muhimmanci, wayar da kan jama’a shi ne ginshiƙin rage yawan aikata laifuka. Ya bayyana cewa kamfen din ba zai tsaya a Abuja kaɗai ba, domin zai kai ga makarantu, da kasuwanni, da al’ummomi a dukkan sassan Nijeriya. A cewarsa, “Manufar ita ce mu kai saƙon har kowane lungu da saƙo na ƙasar nan.”
Ya ƙara da cewa wannan tafiya ta wayar da kai wani “yunƙuri ne na sauya ɗabi’a a ƙasa”, domin tunatar da ƴan ƙasa cewa laifukan yanar gizo kamar zamba, da satar bayanai, da cin zarafi ta intanet suna da illoli masu yawa ga tattalin arziƙi da tsaron ƙasa. Ya gargaɗi matasa da su yi amfani da basirarsu wajen ƙirƙire-ƙirƙire da kasuwanci, ba wajen damfara ba.
A nata jawabin, Barr. Tessy Nnalue, wadda ta wakilci Daraktan Hukumar NOA, ta tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da yaɗa wannan kamfen a rediyo, da talabijin, da fassara shi a harshen gida, da wuraren tarukan al’umma.