Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da sababbin cibiyoyi guda uku na zamani domin kula da masu fama da cutar daji (cancer) a sassa daban-daban na ƙasar nan.
Cibiyoyin sun haɗa da na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Benin (UBTH) a Jihar Edo, Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Katsina, da kuma Asibitin Koyarwa na Jami’ar Nijeriya (UNTH) da ke Enugu.
- Farfesa Yilwatda Ya Zama Sabon Shugaban Jam’iyyar APC Na Ƙasa
- Tsibirin Ciniki Maras Shinge Na Hainan Na Ci Gaba Da Jawo Hankalin Jarin Waje
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafin sa na X, inda ya ce wannan cigaba wani ɓangare ne na shirin farfaɗo da harkar lafiya da gwamnatin Shugaba Tinubu ke aiwatarwa a faɗin ƙasar nan.
A cewar ministan, shi da sauran abokan aikin sa, Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate, da Ministan Kuɗi, Mista Wale Edun, sun halarci bikin ƙaddamar da ɗaya daga cikin manyan ayyukan, wanda ya gudana a Jihar Katsina.
Cibiyoyin da aka ƙaddamar na cikin zagaye na farko na shirin gina sababbin cibiyoyin maganin ciwon daji guda shida a manyan Asibitocin Koyarwa na Tarayya a ƙasar nan.
Wannan cigaba wani muhimmin mataki ne wajen rage wahalar da marasa lafiya ke fuskanta wajen samun ingantacciyar kulawa, da kuma hana fita ƙasashen waje don neman magani.
Gwamnatin ta tabbatar da cewa sauran cibiyoyin da suka rage za su kammala nan ba da jimawa ba domin cika alƙawarin samar da ingantaccen tsarin lafiya ga kowa da kowa a Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp