ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, June 28, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

by Sulaiman
11 months ago
Daji

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da sababbin cibiyoyi guda uku na zamani domin kula da masu fama da cutar daji (cancer) a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Cibiyoyin sun haɗa da na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Benin (UBTH) a Jihar Edo, Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Katsina, da kuma Asibitin Koyarwa na Jami’ar Nijeriya (UNTH) da ke Enugu.

ADVERTISEMENT
  • Farfesa Yilwatda Ya Zama Sabon Shugaban Jam’iyyar APC Na Ƙasa
  • Tsibirin Ciniki Maras Shinge Na Hainan Na Ci Gaba Da Jawo Hankalin Jarin Waje

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafin sa na X, inda ya ce wannan cigaba wani ɓangare ne na shirin farfaɗo da harkar lafiya da gwamnatin Shugaba Tinubu ke aiwatarwa a faɗin ƙasar nan.

LABARAI MASU NASABA

Sace Ɗalibai: Gwamnatin Oyo Ta Sanya Dokar Hana Fita A Ƙananan Hukumomi 10

Iran Ta Jaddada Cewa Ba Ta Da Wani Shiri Na Bada Damar Binciken Wuraren Nukiliyarta

A cewar ministan, shi da sauran abokan aikin sa, Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate, da Ministan Kuɗi, Mista Wale Edun, sun halarci bikin ƙaddamar da ɗaya daga cikin manyan ayyukan, wanda ya gudana a Jihar Katsina.

Cibiyoyin da aka ƙaddamar na cikin zagaye na farko na shirin gina sababbin cibiyoyin maganin ciwon daji guda shida a manyan Asibitocin Koyarwa na Tarayya a ƙasar nan.

Wannan cigaba wani muhimmin mataki ne wajen rage wahalar da marasa lafiya ke fuskanta wajen samun ingantacciyar kulawa, da kuma hana fita ƙasashen waje don neman magani.

Gwamnatin ta tabbatar da cewa sauran cibiyoyin da suka rage za su kammala nan ba da jimawa ba domin cika alƙawarin samar da ingantaccen tsarin lafiya ga kowa da kowa a Nijeriya.

Daji
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sace Ɗalibai: Gwamnatin Oyo Ta Sanya Dokar Hana Fita A Ƙananan Hukumomi 10
  • Sulaiman
    Iran Ta Jaddada Cewa Ba Ta Da Wani Shiri Na Bada Damar Binciken Wuraren Nukiliyarta
  • Sulaiman
    Ribar Manyan Kamfanonin Sin Ta Karu Da Kashi 18.8% Cikin Watanni Biyar Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    An Raba Jadawalin Gasar Premier Ta Ingila Ta Kakar Wasan 2026/2027

MASU ALAKA

Sace Ɗalibai: Gwamnatin Oyo Ta Sanya Dokar Hana Fita A Ƙananan Hukumomi 10
Labarai

Sace Ɗalibai: Gwamnatin Oyo Ta Sanya Dokar Hana Fita A Ƙananan Hukumomi 10

June 27, 2026
Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Fahimtar Juna Da Aka Cimma Tsakanin Amurka Da Iran
Labarai

Iran Ta Jaddada Cewa Ba Ta Da Wani Shiri Na Bada Damar Binciken Wuraren Nukiliyarta

June 27, 2026
ADC Ta Yi Allah-Wadai Da Soke Rajistar NDC, Ta Yi Gargaɗi Kan Barazanar Dimokuraɗiyya
Labarai

ADC Ta Yi Allah-Wadai Da Soke Rajistar NDC, Ta Yi Gargaɗi Kan Barazanar Dimokuraɗiyya

June 27, 2026
Next Post
Anacláudia Rossbach: Ya Kamata Kasashen Afirka Su Koyi Darasi Daga Sin Na Kawar Da Talauci Da Kyautata Kauyuka Zuwa Birane

Anacláudia Rossbach: Ya Kamata Kasashen Afirka Su Koyi Darasi Daga Sin Na Kawar Da Talauci Da Kyautata Kauyuka Zuwa Birane

LABARAI MASU NASABA

Sace Ɗalibai: Gwamnatin Oyo Ta Sanya Dokar Hana Fita A Ƙananan Hukumomi 10

Sace Ɗalibai: Gwamnatin Oyo Ta Sanya Dokar Hana Fita A Ƙananan Hukumomi 10

June 27, 2026
Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Fahimtar Juna Da Aka Cimma Tsakanin Amurka Da Iran

Iran Ta Jaddada Cewa Ba Ta Da Wani Shiri Na Bada Damar Binciken Wuraren Nukiliyarta

June 27, 2026
Ribar Manyan Kamfanonin Sin Ta Karu Da Kashi 18.8% Cikin Watanni Biyar Na Farkon Bana

Ribar Manyan Kamfanonin Sin Ta Karu Da Kashi 18.8% Cikin Watanni Biyar Na Farkon Bana

June 27, 2026
Yaushe Za A Gane Kungiyar Da Za Ta Lashe Gasar Premier?

An Raba Jadawalin Gasar Premier Ta Ingila Ta Kakar Wasan 2026/2027

June 27, 2026
Tsarin Kirkire-Kirkire Na Sin Na Kara Kuzari Ga Makomar Masana’antun Duniya

Tsarin Kirkire-Kirkire Na Sin Na Kara Kuzari Ga Makomar Masana’antun Duniya

June 27, 2026
Kofin Duniya

Daga 1930 Zuwa 2026: Yadda Aka Buga Wasa Na Dubu Ɗaya A Gasar Kofin Duniya

June 27, 2026
Wakilin Sin: Kar A Bari Sabon Nau’in Ra’ayin Nuna Karfin Soja Ya Haifar Da Karin Tasiri

Wakilin Sin: Kar A Bari Sabon Nau’in Ra’ayin Nuna Karfin Soja Ya Haifar Da Karin Tasiri

June 27, 2026
Manoma Sun Nemi Tinubu Ya Kara Yawan Tallafin Noma 

Ko Shirin Da Gwamnatin Jihar Katsina Ke Yi Wa Manoma Zai  Amfane Su A wannan Daminar?

June 27, 2026
CDC Ta Afirka Ta Yaba Da Goyon Bayan Da Sin Ta Bayar Da Hadin Gwiwa Mai Karfi Wajen Yaki Da Ebola

CDC Ta Afirka Ta Yaba Da Goyon Bayan Da Sin Ta Bayar Da Hadin Gwiwa Mai Karfi Wajen Yaki Da Ebola

June 27, 2026
Firaministan Guinea Ya Yabi Kasar Sin Bisa Shawarwarin Da Ta Gabatar

Firaministan Guinea Ya Yabi Kasar Sin Bisa Shawarwarin Da Ta Gabatar

June 27, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.