Gwamnatin Tarayya ta amince da sabuwar allurar rigakafin zazzabin cizon sauro daga Jami’ar Oxford, inda ta zama kasa ta biyu bayan Ghana a duniya da ta amince da hakan.
Alurar rigakafin-R21/Matrix-M, Jami’ar Oxford ce ta habaka kuma Cibiyar Serum ta Indiya ta kera.
- Ma’aikatan Filin Jirgin Saman Legas Sun Shiga Yajin Aiki
- INEC Ta Raba Muhimman Kayyayakin Zabe Don Kammala Zaben Gwamnan Kebbi
Darakta Janar na Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC), Mojisola Adeyeye, ta sanar da ci gaban a Abuja.
Kamar Ghana, Mojisola Adeyeye ta ce an yi allurar rigakafin cutar zazzabin cizon sauro ga yara daga ‘yan watanni biyar zuwa watanni 36.
Ta kara da cewa Nijeriya na sa ran samun akalla allurai 100,000 na alluran rigakafin nan ba da dadewa ba kafin amincewar kasuwa ta fara yin wasu shirye-shirye da hukumar kula da lafiya matakin farko ta kasa.
Alurar rigakafin R21/Matrix-M ita ce ta biyu da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ta amince da ita kuma ta farko da ta wuce matakin na WHO na kashi 75 cikin dari sama da watanni 12 na bin diddigin.
Allurar rigakafin ta nuna ingancin kariyar kashi 77 cikin 100 na tsawon watanni 12 a cikin gwaji na kashi 2b wanda ya shafi kananan yara a yammacin Afirka, biyo bayan alluran kashi uku na farko.
Alurar rigakafin zazzabin cizon sauro na farko, RTS, S ko mosquirix, daga mai yin magunguna na Birtaniya GSK, Hukumar lafiya ta Duniya ta amince da ita a 2021 bayan shekaru da yawa na aiki.
Amma rashin kudi ya hana kamfanin samar da allurai masu yawa kamar yadda ake bukata.
Lokacin da aka amince da maganin sauro, WHO ta ce ta samo asali ne daga sakamakon shirin gwajin da ake yi a kasashen Ghana, Kenya da Malawi wanda ya kai fiye da yara 800,000 tun daga shekarar 2019.