Sakataren zartarwa na Hukumar kula da ziyarar ibada ta Kiristocin Nijeriya (NCPC), Bishop Stephen Adegbite, ya tabbatar da cewa za a ci gaba da gudanar da ziyara ibada ta Kiristocin Nijeriya zuwa kasar Isra’ila da Jordan a watan Satumba mai zuwa, biyo bayan dakatar da ziyarar da aka yi saboda tashe-tashen hankula a yankin Gabas ta Tsakiya.
Adegbite ya kuma ce rabin adadin kudin tafiyar ne kawai za su biya domin gwamnatin tarayya ta bayar da tallafin kashi 50 cikin 100.
- Ministan Yaɗa Labarai Ya Taya Janar Babangida Murnar Cika Shekaru 84
- PDP Ta Ƙalubalanci Sakamakon Zaɓen Cike Gurbi Na Garki/Babura A Jigawa
In ba a manta ba, a baya mun rahoto cewa, a baya hukumar ta sanar da cewa ba za a sake gudanar da ziyarar ibadar ba har sai an warware rikicin Isra’ila da Iran.
Sai dai da yake zantawa da wakilin jaridar PUNCH a ranar Asabar din da ta gabata, Adegbite ya tabbatar da cewa an dage dakatarwar kuma za a ci gaba da gudanar da ziyarar ibadar a watan Satumba.
“Ni da kaina na shiga Isra’ila, na dawo a makon jiya, na tafi tare da wasu ‘yan majalisar wakilai, lallai komai ya lafa.
“Don haka babu wani abin fargaba, za mu fara aikin ziyarar ibada daga watan Satumba,” in ji Adegbite.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp