Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta fara sayar da tan 30,000 na shinkafar a farashi mai rahusa na Naira 40,000 kan buhu mai nauyin kilogiram 50.
Ministan Noma, Sanata Abubakar Kyari, ne ya Æ™addamar da wannan shirin a jiya Alhamis a Abuja. Ya jaddada cewa raba shinkafar yana gudana a fadin Æ™asa don magance Æ™alubalen tattalin arziki da ke shafar ‘yan Najeriya a yanzu.
- Ƴansanda 2 Sun Mutu, 3 Sun Jikkata Bayan Arangama Da Ƴan Shi’a A Abuja
- An Kama ‘Yan Shi’a 97 Kan Kisan ‘Yansanda 2 Abuja
Kyari ya bayyana cewa wannan tallafin abincin umarni ne da shugaba Bola Tinubu don tabbatar da cewa ‘yan Æ™asa ba su ji yunwa ba a wannan lokacin rikicin farashin abinci na duniya da bayan annobar COVID-19, da yaÆ™in Rasha da Ukraine, da canjin yanayi suka haddasa. Ya kuma tabbatar da cewa an samar da matakan da za su tabbatar da gaskiya da daidaito wajen raba shinkafar.
Gwamnati ta aiwatar da tsari na tabbatar da wanda zai sayi shinkafar mai tsauri don hana sayen sama da daya da kuma tabbatar da kowa ya samu daidai, inda za a buƙaci masu sayen su yi rijista da Lambar shaidar ɗan ƙasa (NIN) da lambar wayarsu. Kowanne mutum an yarda ya sayi buhu daya ne na kilogiram 50 kacal.
Kyari ya roÆ™i ‘yan Æ™asa da su haÉ—a kai da hukumomin gwamnati da ke kula da wannan aikin don tabbatar da nasarar sa.