Hukumar kula da hada-hadar hannayen jari ta Nijeriya (SEC), ta fara binciken wasu kamfanoni 79 da ake zargi da damfarar mutane ta hanyar alƙawarin ninka musu kuɗin da suka zuba.
Wannan nau’in damfara ana kiransa da suna Ponzi scheme.
- Buhari Ya Taimake Ni Lokacin Da Wasu Ke Ƙoƙarin Ruguza Majalisar Tarayya — Gbajabiamila
- Za A Ci Gaba Da Zaman Makokin Buhari A Abuja – Garba Shehu
SEC ta ce tana ƙoƙarin wayar da kan jama’a a sassa daban-daban na ƙasar nan kamar kasuwanni da masallatai domin hana mutane faɗawa cikin tarkon masu yaudarar jama’a.
Duk da haka, masana a fannin tsaron intanet sun ce har yanzu gwamnati tana buƙatar ƙara ƙaimi domin mutane da dama har yanzu suna faɗawa cikin irin waɗannan damfara.
Ɗaya daga cikin kamfanonin da ake bincika shi ne FF Tiffany, wanda ake zargin ya yaudari dubban mutane a Nijeriya da ƙasashen waje.
Hukumar SEC ta ce za ta bayyana sakamakon binciken da ta ke yi a nan gaba.
SEC, ta bayyana irin wannan damfara a matsayin barazana ga amincewar jama’a da harkar zuba jari a ƙasar.
Wannan zai iya hana masu kuɗi yadda su zuba jari.
Dakta Nasir Baba Ahmed, masani a harkar tsaron intanet, ya ce akwai wasu alamu da mutane za su iya lura da su domin gane irin waɗannan damfara.
Hukumar SEC ta ce ta himmatu wajen daƙile duk wani shirin damfara a Nijeriya, kuma tana buƙatar jama’a su bincika shafinta na intanet kafin su zuba kuɗi a kowane kamfani.
Haka kuma, hukumar ta ce shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya rattaba hannu a kan wata doka da za a hukunta duk wanda aka kama da irin wannan damfara da tarar Naira miliyan 20 ko kuma zaman gidan yari na shekara 10.
Dakta Nasir, ya ce dole gwamnati ta aiwatar da wannan doka da kyau, tare da ɗaukar wasu ƙarin matakai domin daƙile wannan matsala gaba ɗaya.
A watan Afrilu na wannan shekara ma, mutane da dama sun yi asarar kuɗi a wani tsarin zuba jari da ake kira CryptoBank Exchange (CBEX) inda aka ce an yi asarar aƙalla Naira tiriliyan ɗaya.
Ko da yake hukumomi sun fara bincike, har yanzu sun ce da wuya a iya dawo da kuɗin jama’a.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp