Gwamnatin tarayya ta bayyana nasarorin da ta samu a ƙoƙarinta na yaƙi da cin hanci da rashin tsaro a faɗin Nijeriya. A cewar Darakta-Janar na hukumar wayar da kan jama’a (NOA), Mallam Lanre Issa-Onilu, an karɓo Naira biliyan 21, kuma an kashe ƴan ta’adda 78, sannan an daƙile asarar fiye da Naira biliyan 319 sakamakon gobara.
Issa-Onilu ya bayyana hakan ne a yayin taron manema labarai na haɗin gwuiwar hukumomin tsaro da aka gudanar a watan Agusta a Abuja. Ya ce an samu waɗannan nasarori ne sakamakon haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro, daga Arewa maso Gabas har zuwa yankin Niger Delta.
- AFCON 2023: Hukumar NOA Ta Tsunduma Gangamin Tara Wa Super Eagles Ɗimbin Magoya Baya – Minista
- Shirin Sabunta Fata Na Tinubu Yana Samar da Damarmakin Cigaba — Minista
A cewar sa, rundunar ƴansanda ta gudanar da ayyuka 326 inda aka kama mutane 2,109 tare da ceto waɗanda aka yi garkuwa da su. Haka kuma, an tarwatsa ƙungiyoyin safarar makamai guda shida, tare da kashe ƴan ta’adda 78 a yayin hare-haren yaƙi da ta’addanci.
Baya ga haka, hukumar NDLEA ta kwace ƙwayoyi masu nauyin kilo miliyan 2.9, ciki har da tramadol kilo 520 da methamphetamine kilo 7.35. An kuma warware rikice-rikicen al’umma 720 ta NSCDC, yayin da hukumar FRSC ta ruwaito mutuwar mutane 2,838 a haɗarran hanya.
Hukumar ICPC kuwa ta karɓo ₦21bn da dala miliyan ɗaya, tare da gudanar da taruka 352 don faɗakar da jama’a kan cin hanci. A bangaren tsaron iyaka, an ceto mutane 82 daga safarar mutane, an dawo da 495, tare da karɓar ƴan Nijeriya 110 da aka deporto daga Saudiyya. NOA ta ce waɗannan nasarori na nuna ci gaba a ƙoƙarin da gwamnati ke yi na dawo da martabar tsaro da amintar jama’a.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp