Gwamnatin Tarayya ta mayar da martani akan zargin da gwamnan jihar Kaduna, mal. Nasir Ahmed El-rufai ya yi na cewa wasu a fadar shugaban kasa na shirya wa dan takarar shugaban kasa a jamiyyar APC sanata Bola Ahmed Tinubu makarkashiya.Â
El-rufai ya yi wannan zargin ne yau laraba a hirar da ya yi da gidan talabijin na Channels.
Gwamnatin ta mayar da martanin ne ta hanyar ministan yada labarai da al’adu Alh Lai Mohammed.
Mohammed, a hirarsa da manema labarai na fadar shugaban kasa a yau laraba jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwar kasar wadda shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta ya nanata cewa, gwamnatin Buhari ta mayar da hankali ne don ganin an gabatar da ingataccen zabe a 2023.
Ministan ya ce, idan har akwai wani da ke kitsa wa wani dan takara makarkashiya, gwamnatin tarayya ba ta da masaniyar hakan a hukumance.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp