Gwamnatin tarayya ta raba kayayyakin abinci da yawansu ya kai buhu dubu hudu da dari biyu (4,200) ga al’ummar jihar Bauchi domin rage kaifin talauci da fatara a tsakanin al’umma.
Kayan abincin sun kunshi buhun Dawa 1,200, buhun Masara 1,200, buhunan Garin Kwaki 1,200 da kuma Gero buhu 600 domin raba wa marasa karfi a cikin al’umman jihar.
Da take mika kayayyakin a sakatariyar APC da ke Bauchi, karamar ministan ma’aikatar kasuwanci da masana’antu da zuba hannun jari, Ambasada Mariam Yalwaji Katagum, ta ce, tallafin an yi ne domin rage wa mutanen da suke fama da wahalar rayuwa dawainiyar da suke ciki.
Ministar wacce ta samu wakilcin babban mai bada shawara, Dakta Ahmad Mabudi, ta misalta tallafin a matsayin wani bangare na kokarin shugaban kasa Muhammadu Buhari na cire miliyoyin mutane daga kangin talauci da fatara.
“Babbar fatanmu a nan shine a tabbatar an yi adalci wajen rabon, kuma ina jawo hankalin masu kula da rabon da su tabbatar sun yi adalci domin wadanda suka cancanta su samu daga kowace jam’iyya kuma mutum ya fito ba wai zallar ‘yan APC ba.”
Katagum ta jinjina wa jagororin jam’iyyar APC na jihar Bauchi bisa kokarin da suka yi wajen ganin an samu nasarar kawo wannan tallafin.
A nasa bangaren, shugaban jam’iyyar APC na jihar Bauchi Alhaji Babayo Aliyu Misau, wanda ya samu wakilcin sakataren jam’iyyar, Mustapha Zirami, ya ce, an samar da kayan abincin ne da nufin raba wa ga marasa karfi da suke fadin jihar.
Ya kuma ce, za a rabar da kayan abincin ne ga kowani bangare ba tare da la’akari daga wacce jam’iyya mutum ya fito ba.
Ya gode wa ministar bisa wannan abinci da ta yi tsayuwar daka wajen kawo shi jihar, sai ya jawo hankalin masu alhalin rabon da su ji tsoron Allah kada su sanya son zuciya wajen yin rabon.