Ma’aikatar ayyuka ta tarayya ta kammala gyaran sashi na 2 na hanyar Kano zuwa Maiduguri a jihar Bauchi wacce a kwanakin baya mummunar ambaliyar ruwa ta katse, inda ta bude hanyar ga matafiya.
Ministan ayyuka, David Umahi, ne ya sake buɗe hanyar bayan kammala aikin gyaranta don sauƙaƙa zirga-zirgar ababen hawa ga masu bin hanyar.
- Wakilin Sin Ya Yi Kira Da A Kara Azama Wajen Warware Rikicin Sudan Ta Hanyar Siyasa
- A Shirye Sin Take Ta Tsara Yarjeniyoyin Ciniki Cikin ’Yanci Da Karin Kasashe Masu Tasowa
A kwanakin baya dai, LEADERSHIP ta ruwaito cewa, wata mummunar ambaliyar ruwa da ta afku sakamakon mamakon ruwan sama ta lalata Sashi na biyu a Sabon Gari da ke kan babbar hanyar Kano zuwa Maiduguri a jihar Bauchi.
Cikin wata sanarwa da mai bai wa ministan shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Orji Uchenna Orji, ya fitar, ya ce ambaliyar ruwa da sauyin yanayi ya haifar ya sanya al’ummar yankin da lamarin ya shafa cikin kunci da saura masu amfani da hanyar wanda haka ya sa shugaban kasa Bola Tinubu ya bayar da umarnin fara gyaran cikin gaggawa.
Ya kara da cewa, a ci gaba da ƙoƙarin shugaban ƙasa, Ministan Ayyuka, Nweze David Umahi, ya ziyarci yankin a ranar 15 ga watan Agustan 2024, inda ya kaddamar da agajin gaggawa na matakan magance matsalolar da ya shafi hanyar na gyara ta.