Fadar shugaban kasa ta shiga tsakanin rikicin da ya kunno kai tsakanin gwamnatin Jihar Kogi da attajirin Afirka, Aliko Dongote, dangane da mallakar katafaren kamfaninsa na siminti da ke Obajana.
Bayanai sun ce an gana tsakanin shugaban rukunonin kamfanin na Dongote da kuma gwamnan Jihar Kogi, Yahya Bello da kuma takwaransa na Jihar Nasarawa Abdullahi Sule.
- An Saka Ranar Bikin Nadin Sarki Charles lll A Matsayin Sabon Sarkin Ingila
- Majalisar Dokokin Kano Ta Amince A Sauya Sunan Jami’ar KUST Zuwa Sunan Dangote
Yukurin sulhun da fadar shugaban Nijeriya ta yi, ya zo ne, bayan matakin da gwamnatin Kogi ta dauka na rufe katafaren kamfanin simintin na Obajana, bisa zargin kauracewa biyan haraji, da kuma rashin fayyace gaskiyar hakkin mallakar kamfanin.
Wasu majiyoyi sun rawaito cewar shugabannin rukunin kamfanonin na Dangote sun kammala shirin tunkarar kotu a wannan makon kan al’amarin, ciki kuwa har da yadda ‘yan banga na gwamnatin Jihar Kogi suka kai farmaki kan katafariyar masana’antar simintin da ke Obajana, inda ake zargin sun jikkata ma’aikata da dama tare da rufe kamfanin.
A ranar Alhamis din da ta gabata, gwamnatin Kogi, ta gabatar da rahoton kwamitin kwararru na musamman kan tantance halaccin mallakar kamfanin simintin na Obajana.
Yayin gabatar da rahoton, sakatariyar gwamnatin Kogi Misis Folashade Ayoade, ta ce ba a bi ka’ida ba wajen mika Obajana zuwa kamfanin Dangote.
Sannan wasu takardun shaida guda uku da suka tabbatar da cewa gwamnatin Kogi ce ta mallaki kamfanin simintin na Obajana , an yi amfani da su wajen karbar bashin Naira biliyan 63 da Dangote ya yi.