Gwamnatin tarayya a karkashin ma’aikatar aikin gona ta kasa ta tallafa wa manoman alkama a jihar Katsina da ingantaccen irin alkama buhu biyu mai cin kilo hamsin hamsin da buhun taki 10 da maganin feshi na kashe ciyawa tare da takin zamani na ruwa wanda kundisu ya kai naira dubu 300,000, manoman za su biya kashi 50 bisa 100 na kudin ana karbar dubu 180,500 nan take kafin su dauki kayan, an kasa manoman alkaman zuwa shiyoyi bakwai a fadin jihar, a shiyyar Malumfashi ta kunshi kananan hukumomi 5, kananan hukumomin sune Kafur, Kankara, Bakori, Danja da karamar hukumar Malumfashi. Inda manoma 653 za su amfana da shirin a shiyyar Malumfashi, kanfanin Agro Dealer shi ne kanfanin SHALTEN ne ya samar da ingantattun kayan jagoran kanfanin Malam Ibrahim Muhammad wanda ake kira da Big G Funtuwa ya tabbatar wa manoman kanfanin su ya kawo ingantaccen iri da taki mai kyau da sauran kayayyaki.
Malam Ibrahim ya yaba wa gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa Alhaji Bola Ahmed Tinubu wajen inganta noma a kasar nan, ya ce, shirin ya sha banban da sauran shirin da aka taba yi wajen bunkasa noma musamman noman alkama, ya ce gwamnatin tarayya da gaske take wajen kawo karshen tsadar matsalar abinci.
Wasu daga cikin manoman da suka fito daga kananan hukumomi Kafur, Malumfashi da Danda, Alhaji Garba da Hajiya Hadiza Muktar Malumfashi sun yaba wa gwamnatin tarayya wajen kawo wannan shirin na tallafa wa manoma don haka suna kira ga gwamnati da ta ci gaba bunkasa shirin sun kuma yaba wa kanfanin da ya samar da kayan sobada ingantattu ne masu kyau.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp