A halin yanzu gwamnatin tarayya da bayar da umarnin sake sayar da wasu kamfanonin samar da wutar lantarki 4 ta kuma umarci a sake rarraba wasu kamfanonin zuwa kananan kamfanoni saboda girmansu ya na kawo cikas ga yadda suke gudanar da ayyukansu.
Sanarwar ta kuma ce gwamnati ba za ta janye sayar da kamfanonin da ta yi ba amma za a sake rarraba su don su samu yin aiki yadda ya kamata, al’umma su amfana da ayyukansu ba kamar yadda lamarin yake a halin yanzu ba.
- Matsalar Tsaro: Gwamnan Zamfara Ya Nanata Bukatar Amfani Da Fasahar Zamani
- Zargin Badakala: Tataburzar EFCC Da Yahaya Bello Na Daukar Sabon Salo
Wannan kuma yana zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin a sayar da wasu kamfanoni samar da wutar lantarki 4 (Discos) wadanda bankuna da kamfanin AMCON suka karbe ragamar tafiyar da su saboda basuka.
Bankin UBA ne ta karbe harkokin kamfanin samar da wuta na Abuja yayin da bankin Fidelity Bank ya karbe harkokin kamfanin samar da wuta na Benin da Kaduna da na Kano. Sai kuma kamfanin samar da wuta na Ibadan da ya koma karkashin kamfanin AMCON. An yanke wa wadannan kamfannnin hukuncin ne saboda sun kasa biyan kudaden da wadannan bankuna ke binsu.
Gwamnati ta bayyana cewa, wadanda suka sayi kamfanonin a lokacin da aka yi gwanjon su ne tunda farko a shekarar 2013 ne basu da kudi da kuma kwarewar da ake bukata na tafiyar da kamfanoni irin wannan.
Wannan ma yana zuwa ne a yayin da majalisar dattawa ta caccaki kamfanonin Discos a kan rashin iya aiki tun da aka sayar musu da kamfanonin a shekara 10 da suka wuce.
A jawabinsa a yayin da ‘yan kwamitin majalisar dattawa a kan wutar lantarki a karkashin jagorancin Sanata Eyinnaya Abaribe, suka kai masa ziyara, Ministan wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa, a halin yanzu gwamnatin tarayya ta fara aikin sake fasalin kamfanonin samar da wuta 11 na kasar nan.
Ya ce, akwai ayyyuka fiye da 100 da kamfanonin suka bayar amma fiye da shekara 23 da suka wuce amma har yanzu ba a kammala ba.