Da yiyuwar gwamnatin tarayya za ta aiwatar da wani bincike na musamman kan wasu harkokin addinai da ke haifar da tashin-tashina na addini a wasu sassan kudu maso yammacin kasar.
A wani binciken da majiyarmu ta gudanar, ya tabbatar mata da cewa gwamnatin tarayya ta nuna damuwarta matuka kan rahotonnin aikace-aikacen da ake samu na wasu kungiyoyin masu tsattsaurar ra’ayi da tashin hankali na addini.
- Bajintar Aiki: Majalisar Dattawa Ta Jinjina Wa Ministan Yaɗa Labarai
- Yakin Haraji Da Gwamnatin Amurka Ke Gudanarwa Na Jefa Fargaba a Zukatan Amurkawa
A baya-bayan nan wasu lamura biyu sun wakana a Jihar Oyo wanda ake zargin masu tsattsaurar ra’ayi ne suka haifar da ke tasiri a shiyyar kudu maso yamma, wanda kai tsaye aka fahimci ka iya janyo tashin hankali mai tsauri na addini.
Majiyoyi masu tushe sun tabbatar da cewa an sanar da hukumomin tsaro wadannan aikace-aikacen da ake zargin na masu tsautsaurar ra’ayin ne a kudu maso yammacin kasar domin neman daukan matakan gaggawa.
Majiyoyin sun ce tunin aka bayar da umurni ga jami’an tsaro da su bi sawun lamarin a sirrance domin kawo karshen matsalar tun kafin ta yi kamari.
Wata majiya ta ce baya ga barazanar kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi da ‘yan ta’adda da ke kokarin kutsawa yankin ta tsohon gandun dajin Oyo da dajin Kamoko, wanda ya taso daga jihohin Kaduna da Neja da Kwara da kuma dajin Oyo, akwai rahotannin da ke cewa, wasu kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi suma suna yunkurin shiga yankin Kudu maso Yamma da yada kiyayya ta addini.
An kuma gano cewa jami’an tsaron sun fara binciken wata kungiyar da ke yunkuri kan shari’a wacce a baya-bayan nan ta yi barazanar kafa kotun shari’a a cikin Oyo. Majiyoyin sun ce makonnin da suka gabata jami’an tsaro sun yi tambayoyi ta mutane da dama da suke da alaka da shirin kafa shari’a a Oyo.
Haka kuma an gano cewa yunkurin masu shari’a shi ne don su kafa majalisar shari’a da za ta kula da wasu harkokin jama’a kamar aure, sakin aure da gado, saboda sun fahimci kotunan da ke akwai a halin yanzu sun aminta ne da harkokin kwansitushin.
A halin da ake ciki kuma, jam’iyyar ‘Oodua People’s Congress’ (OPC) karkashin Fredrick Fasheun, ta bukaci daukacin gwamnonin Kudu maso Yamma shida da su dauki matakin gaggawa na tsaro wajen tarwatsa sansanonin ‘yan ta’adda da ke fitowa daga Arewa, a cikin dazuzzukan Yarbawa, tare da yin alkawarin taimaka wa jami’an tsaro wajen magance matsalar barazanar ba tare da bata lokaci ba kafin a makara.
OPC a wata sanarwar da ta fitar, ta ce, a shirye take kuma akwai zaratan da za su taimaka wa jami’an tsaro wajen kawo karshen wadanda ake zargin ‘yan ta’adda ne da suke kwararowa daga arewa zuwa kudu.