Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya tabbatar da cewa gwamnati za ta yi duk abin da ya dace don ceto ‘yan matan da aka sace a Makarantar Government Girls Secondary School, Maga, a Jihar Kebbi.
Da yake magana a Birnin Kebbi bisa umarnin Shugaba Bola Tinubu, Shettima ya ce sace yaran tashin hankali ne ga dukkanin ‘yan Nijeriya.
- Binciken CGTN: Akwai Yiwuwar Firaministar Japan Ta Zama “Mai Aikata Laifin Yaki” Bisa Yunkurinta Na Keta Dokoki
- Gwamnatin Netherlands Ta Dakatar Da Nuna Iko A Kamfanin Nexperia
Ya kuma ce waɗanda suka kashe Birgediya Janar Musa Uba da mataimakin shugaban makarantar za su fuskanci hukunci.
Ya isar da saƙon ta’aziyyar Shugaba Tinubu ga iyayen yaran da aka sace da kuma al’ummar Jihar Kebbi.
Shettima ya tabbatar musu cewa Nijeriya ba za ta bari su su yi kuka su kaɗai ba, kuma gwamnati za ta ci gaba da aiki har sai an dawo da yaran lafiya.
Ya kuma yaba wa jami’an tsaro, Gwamnan Jihar Kebbi Nasir Idris, masu ruwa da tsaki, da ƙungiyoyin sa-kai bisa irin gudunmawar da suke bayarwa.
Gwamna Idris ya gode wa Shugaba Tinubu bisa goyon baya, sannan ya bayyana cewa yana da ƙwarin gwiwa cewa za a kuɓutar da ‘yan matan nan ba da jimawa ba.














