Biyo bayan harin bam da aka kai kauyen Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna, Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa, Gwamnatin tarayya za ta sake gina wa mazauna kauyen gidaje, Makaranta da Asibiti sannan kuma za ta samar musu da kayan Noma.
Shi ma, Gwamna Uba Sani ya baiwa iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su tallafi, inda ya ce, gwamnati za ta dauki nauyin kudin duk abinda ake bukata wajen jinya ga wadanda suka jikkata kuma ake duba lafiyarsu a asibitin koyarwa na Barau Dikko da ke jihar Kaduna.
- Ba Za A Cimma Wannan Yarjejeniya Ba Tare Da Taimakon Sin Ba
- A Magance Rashin Aikin Yi A Tsakanin Matasa
Bugu da kari, Gwamnan ya sha alwashin bayar da tallafi na kudi, kula da lafiyar kwakwalwa da kayan masarufi ga marayun da suka rasa masu kula da su a wannan mummunan lamari.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya tarbi wata tawagar jiga-jigan gwamnatin tarayya da suka hada da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, kakakin majalisar wakilai Abbas Tajuddeen, ministan tsaro Mohammed Badaru Abubakar, da shugaban jam’iyyar APC na kasa Dr Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamna Sani ya kuma mika godiyarsa ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta mika ta’aziyyarsa kan ibtila’in inda kuma ya bada umurnin gudanar da bincike cikin gaggawa don gano musabbabin kai harin.
Gwamnan ya kuma tabbatar wa da tawagar cewa, za a bayyanawa Jama’a sakamakon binciken da zarar an kammala, sannan ya jaddada kudirin Shugaba Tinubu na biyan diyya ga iyalan wadanda abin ya shafa tare da kaddamar da sake gina muhimman ababen more rayuwa a cikin al’ummar Tudun Biri.
Acewarsa, “Za a gina gidaje na zamani tare da samar musu da asibiti da kayan noma da makarantu. Don haka, ina godiya ga shugaban kasa da mataimakinsa”, inji Gwamna Sani.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, wanda ya wakilci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya mika sakon jajensu tare da nuna goyon bayansu ga gwamnati da al’ummar Kaduna a wannan lokaci mai cike da damuwa.