A yau Talata ne gwamnatin tarayya za ta kafa wani kwamiti na ma’aikatu domin binciken ayyukan digirin bogi.
Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar ilimi ta tarayya, Ben Goong, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya aikewa manema labarai a Abuja, ya ce za a kaddamar da kwamitin ne da karfe 2 na rana a ranar Laraba.
- NYSC Ta Yi Jimami Kan Kisan ‘Yar Hidimar Kasa A Kaduna
- Jerin Jami’o’i 18 Da NUC Ta Haramta Karatu Acikinsu
LEADERSHIP ta rawaito cewa, batun da ya da baibaye ‘digirin bogi’ ya sake fitowa fili ne bayan wani rahoton bincike da wani dan jarida mai suna Umar Audu ya yi, inda ya bayyana yadda ya samu digiri a cikin makonni shida har ma ya shiga cikin shirin masu yi wa kasa hidima (NYSC).
Goong ya ce, “Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman, a yammacin yau, zai kaddamar da kwamitin ma’aikatu don tattauna batun digirin bogi”
Cikakkun bayanai Daga baya…
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp