Gwamnatin Tarayya ta fito da wasu tsare-tsare waɗanda za su taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasar nan tare da samar da aikin yi.
Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Dakta Doris Uzoka-Anite, ita ce ta bayyana haka a wurin wani taro na musamman da ‘yan jarida wanda Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, a ƙarƙashin minista Alhaji Mohammed Idris, ta shirya a ranar Juma’a a Cibiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa da ke Abuja.
- Durƙushewar Darajar Naira: Atiku Ya Ba Da Mafita Bayan Ya Caccaki Tinubu
- Dennis Francis: Bikin Bazara Kyauta Ce Da Kasar Sin Ta Baiwa Duniya
Taron shi ne na biyu a ci gaba da jagorantar ministoci da Idris ke yi domin su riƙa bayyana wa manema labarai irin ci gaban da suka samar a watanni shida da su ka yi, sai kuma bayyana musu irin alƙiblar da ake fuskanta nan gaba.
Tun da farko, Ministan yada labarai, Idris ya buɗe taron da jawabi inda ya ce: “Mun taru a nan domin gina ginshiƙin yarda, amana a tsakaninmu da ‘yan jarida, ta yadda za mu tabbatar cewa, ana sanarwa jama’a abin da muke aiwatarwa.
“Wannan taro ya ba ku damar ku gana kai-tsaye da manyan jami’an gwamnati, ku yi mana tambayoyin da suka cancanta da waɗanda suka shige wa jama’a a duhu.”
Ministan ya jaddada ƙoƙarin da ma’aikatarsa ke yi wajen yin komai a fili ba tare da ƙumbiya-ƙumbiya ba.
Ya nanata damar samun bayanai da manema labarai ɗin ke da ita, tare da bayyana muhimmiyar rawar da ‘yan jarida ke takawa wajen isar da saƙonni ga jama’a.
Haka kuma ya ƙara nuna ƙoƙarin tabbatar da yaɗa labarai a kusa da nesa, ta hanyar da aka saba da kuma sabbin hanyoyin na’urorin zamani masu kai saƙonni nesa, nan take.
Yayin da ta ke nata jawabin ga manema labaran, Dakta Doris Uzoka-Anite ta zayyana shirye-shiryen bunƙasa tattalin arzikin da ta bijiro da su, waɗanda ta ce, har samar da ɗimbin ayyukan yi ga ɗimbin ‘yan Nijeriya za su yi.
Ta ce dukkan waɗannan shirye-shirye sun ta’allaƙa ne bisa turbar shikashikai takwas na Shirin Shugaban Ƙasa na Fata Nagari, wanda a Turance ake kira ‘Renewed Hope,’ waɗanda su ka haɗa da bunƙasa tattalin arzikin ƙasa, samar da ayyukan yi, samar da jari, samar da yanayin gudanar da kasuwanci mai yalwa, rage fatara da talauci.
Ministar ta ce ma’aikatar ta na nan ta na tattauna yadda Nijeriya za ta samu damar cin gajiyar tsarin gudanar da cinikayya a sauƙaƙe tsakanin ƙasashen Afirka, wato AFCFTA.
Ta ce gudanar da wannan kasuwanci kai-tsaye ba tare da tarnaƙi ba zai faɗaɗa kasuwanci tsakanin ƙasashen Afirka, kuma zai ƙara ba da damar shigowar masu zuba jari.
Ta ce a taron baya-bayan nan na 13 na Ministocin Kasuwanci da Cinikayya na AFCFTA, an jaddada matsayin da Nijeriya ke da shi wajen bunƙasar kasuwanci ta hanyar fasahar zamani, sai kuma ƙoƙarin da ƙasar ke yi wajen daƙile haramtaccen ciniki ta hanyar amfani da jiragen ruwa.