Gwamnatin Jihar Yobe ta sanar da rufe wasu kasuwanni uku na mako-mako na ɗan wani lokaci, saboda tsoron yiwuwar hare-haren Boko Haram.
Kasuwannin da abin ya shafa su ne na Katarko, Kukareta da Buni Yadi, dukkaninsu a Ƙaramar Hukumar Gujba.
- Ɗan Wasan Liverpool, Diogo Jota, Ya Mutu A Hatsarin Mota
- ’Yansanda Sun Ceto Ɗan Ghana, Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane 3
An rufe su ne domin taimakawa aikin da jami’an tsaro ke yi wajen yaƙar ’yan ta’adda a faɗin jihar.
A cewar Mai Bai Wai Gwamnan Yobe Shawara Kan Sha’anin Tsaro, Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam (mai ritaya), an rufe kasuwannin ne don bai wa jami’an tsaro damar gudanar da ayyukansu cikin sauƙi tare da inganta tsaro a yankunan da abin ya shafa.
Ya ce, “Wannan mataki na ɗan lokaci ne da zai taimaka wajen cimma wasu muhimman manufofi na tsaro a jihar.”
Birgediya Janar Abdulsalam ya roƙi jama’a da su bai wa jami’an tsaro haɗin kai, duk da cewa rufe kasuwannin na iya kawo wata matsala ga rayuwar yau da kullum.
“Gwamnati na ƙoƙarin ganin an rage tasirin da rufe kasuwannin ka iya haifarwa ga al’umma. Muna roƙon ku fahimce mu saboda zaman lafiya da tsaro,” in ji shi.
Ya kuma tabbatar wa mazauna yankunan cewa za a sake buɗe kasuwannin nan ba da jimawa ba, idan aka kammala aikin tsaro da ake gudanarwa.
Kasuwannin da aka rufe suna daga cikin manyan kasuwanni a wannan yanki na Jihar Yobe.
Wani mazaunin Kukareta ya shaida wa wakilinmu cewa ba su san dalilin rufe kasuwannin ba, kawai ji suka yi an ce an bayar da umarni daga sama.
Wani ɗan kasuwa daga Buni Yadi da ya nemi a sakaya sunansa ya ce ya ji an ce an rufe kasuwannin ne saboda wasu ’yan kasuwa na sayar wa Boko Haram kayan abinci.
Ya ce, “Ban san da yawa ba, amma abin da na ji shi ne an bayar da umarni a ranar Litinin, suna cewa masu sayar da abinci a waɗannan kasuwanni suna taimakawa Boko Haram wajen siyan kayan abinci.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp