Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya mika gidaje dari hudu da sittin (460) ga kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC) reshen jihar Zamfara, domin rabawa kananan ma’aikata a jihar.
Gwamna Matawalle ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a wajen bikin na mika rukunin gidajen da ke kan titin Gidan Dawa Daza a Gusau, babban birnin jihar.
- 2023: Zan Dora Daga Inda Na Tsaya Idan Na Zarce – Matawalle
- Gwamnatin Zamfara Ta Gano Likitocin Bogi 199 A Jihar
Gwamnan ya bayyana cewa samar da gidajen na daya daga cikin kokarin gwamnatinsa na samar da wurin kwana na dindindin ga ma’aikatan gwamnati a jihar manyan da kananansu”.
“Ya kara da cewa, baya ga samar da gidaje dari hudu da sittin da aka kammala na kananan ma’aikata, za a sake gina wasu gidaje 1000 ga manyan ma’aikatan gwamnati a fadin jihar, inda ya yi nuni da cewa a cikin makon nan ne zai yi bikin kaddamar da harsashin ginin ma’aikatan.
Matwalle ya ce za a gina gidaje dubu daya a Gusau, da nufin magance kalubalen wurin kwana na manyan da kananan ma’aikata a jihar.
“Matawalen ya bayyana matukar damuwarsa kan yadda ma’aikatan gwamnati ke yin ritaya bayan shekaru talatin da biyar suna aiki ba tare da sun mallaki gida ba, wannan ya ce gwamnatinsa za ta magance hakan ta hanyar gina musu gidajan.
A cewar Gwamnan, rukunin farko da na biyu na gidajen da suka kai dari hudu da sittin za a raba su ne ga ma’aikata tare da rage kashi arba’in cikin dari na jimillar kudaden da za a biya cikin shekaru goma.
Gwamna Bello Matawalle ya yi kira ga shugabannin kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC) da su hada kai da ofishin shugaban ma’aikata na jiha da kuma hukumar kula da harkokin kwadago domin tabbatar da adalci wajen rabon gidajen domin amfanar ma’aikatan gwamnati.
Shugaban Kungiyar Kwadago ta Nijeriya, Kwamared Sani Halliru Magajin Rafin Kurya, ya bayyana jin dadinsa ga Gwamnan bisa shirinsa na samar da gidajen kwana ga ma’aikatan da ke aiki.
Kwamared Sani Halliru, a madadin daukacin ma’aikatan jihar ya godewa gwamnan kan yadda ya ceto dubban ma’aikata da iyalansu daga matsalar rashin matsuguni musamman bayan ritayar da suka yi tare da tabbatar wa Gwamna Matawalle goyon bayan ma’aikata da hadin kai domin gwamnatinsa ta samu nasara ga kowa da kowa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp