A halin yanzu gwanatin Jihar Zamfara ta fitar da Naira Biliyan 1 don aikin gyara da fadada aikin samar da ruwan sha a garin Gusau.
Kwamishinan albarkatun ruwa, Alhaji Ibrahim Mayana, ya sanar da haka a lokacin da mataimakin gwamnan jihar Sanata Hassan Nasiha, ya kai ziyara ta musamman ma’aikatar ruwa don gane wa kansa yadda aikin yake tafiya.
Kwamishinan ya kara da cewa, bayan karancin ruwan da aka fuskanta a garin Gusau da kewaye, gwamnati ta karfafa tabbatar da an fuskanci aikin gyara da fadada aikin samar da ruwan sha.
A jawabinsa, mataimakin gwamnan, ya nuna gamsuwarsa da yadda aikin yake tafiya, ya kuma jaddada kudurin Gwamnan Jihar Bello Matawalle na tabbatar da an kawo karshen matsalar ruwan da ake fusanta a garin Gusau da kewaye.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp