Gwamnatocin kananan yankunan Sin, sun fara bayar da katunan rangwamen sayayyar kayayyakin amfanin yau da kullum, a wani mataki na farfado da karsashin kasuwanni, da ingiza hada hadar cinikayya, a gabar da kasar ke sassauta matakan yaki da annobar COVID-19.
A ranar 7 ga watan nan ne aka ayyana wasu matakai 10, na kara inganta yaki da annobar COVID-19 a kasar Sin, matakan dake kunshe da sassauta bukatar yin gwajin cutar, da batun killace masu fama da ita. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan daga CMG Hausa)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp