Daukacin gwamnatocin kasar nan na kamun kafa wurin Shugaban kasa Bola Tinubu domin ganin ba a aiwatar da hukuncin kotun koli na bai wa kananan hukumomi ‘yancin gashin kai.
Wasu gwamnoni a lokacin taro da Shugaba Tinubu a fadarsa da ke Abuja, sun kalubalanci bai wa kananan hukumomi kudadensu kai tsaye daga asusun gwamnatin tarayya, inda suka bukaci a magance bashi na biliyoyin dola da ake bin kananan hukumomin kafin fara aiwatar da tsarin.
- Kotu Ta Dakatar Da INEC Karɓar Buƙatar Yin Kiranye Ga Senata Natasha
- Zargin Kisan Kiristoci A Nijeriya: Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Watsi Da Rahoton Amurka
Ma’aikatan fadar shugaban kasa sun ce gwamnatocin sun yi amfani da damar cin abinci na bude-baki ga shugaban kasa wajen kamun kafa kuma sake tattaunawa game da bai wa kananan hukumomi kudadensu kai tsaye, wanda ya samu tsaiko wajen aiwatar da shi.
Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa a lokacin da gwamnatoci suka zo fadar shugaban kasa a ranar Litinin don yi bude-baki, sun nemi ganawar sirri da shugaban kasa, wanda suka yi a ranar Talata da yamma, wanda ya dauki tsawon lokaci tare da shi.
Da yake magana kan batun wanda ya bukaci a sakaye sunansa domin ba a ba shi damar yin magana ba a hukumance, ya ce, “A karshe sun gana da shugaban a ranar Talata don samun mafita. Suna ta yin kokarin yin kamun kafa wurin shugaban kasa na hana kananan hukumomi samun gashin kai.00 / 1:01
“Abin da ke faruwa shi ne batun abubuwa guda biyu. Gwamnatin tarayya tana son a dunga biyan kudaden kananan hukumomi kai tsaye zuwa Babban Bankin Nijeriya (CBN), kuma ya kamata dukan kananan hukumomi su bude asusu a CBN.
“Amma gwamnoin sun ce a’a. Ba sa son hakan. Sun ce idan kudaden n ya kai ga CBN, ya nuna cewa gwamnatin tarayya ce take kulawa da komi.”
Majiyar ta ce tattaunawar Tinubu da gwamnoni ya bayyana cewa, gwamnonin na bukatar a kai kudaden zuwa bankunan kasuwanci nan take.
“Daya daga cikin gwamnonin ya ce idan har CBN ke kula da asusun, za su bukaci amincewa daga wurin akanta janar na Nijeriya. Wannan yana nufin cewa har yanzu yana karkashin ikon gwamnatin tarayya ne kuma ba su bukatar hakan ya faru. Suna son a kai shi ga banki na kasuwanci. Amma gwamnatin tarayya ta ki amincewa,” in ji majiyar.
Game da sakamakon ganawar, majiyar ta ce, “Sun ce ganawar ta haifar da da mai ido. Amma ban san abin da suka tsaya a kai ba. Suna aiki tare da wasu ma’aikata don su sami hanyar samun fita. Amma abu mafi muhimmanci shi ne, an rike kudaden kananan hukumomi. Ba a biya ba. Saboda wannan dambarwa.”
A tarihi, an dade ana jayayya kan kudaden kananan hukumomi, musamman domin ikon da ke tsakanin jihohi da kananan hukumomi.
A ranar 11 ga Yuli, 2024, kotun koli ta zartar da hukunci mai muhimmanci da ya tabbatar da bai wa dukkan kananan hukumomin kasar nan cin gashin kai.
Ya hukuncin ya bayyana cewa dole ne a biya kudaden kananan hukumomi kai tsaye daga asusun gwamnatin tarayya.
Wannan ya biyo bayan karar da gwamnatin tarayya ta shigar, wadda ta nemi ta daukaka ‘yancin kananan hukumomi kamar yadda kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 ya tanada.
Kotun kolin ta jaddada cewa ba ya saba wa tsarin kundin mulki gwamnonin jihohi su ci gaba da kula da kudaden kananan hukumomi, inda ta bukaci a dunga tura wa kananan hukumomin kudadensu kai tsayi daga asusun gwamnatin tarayya.
Haka kuma hukuncin ya hada da tsarin samar da shugabannin kananan hukumomi ta hanyar dimokuradiyya ne kawai za su iya samun kudadensu kai tsaye daga asusun gwamnatin tarayya.
An samar da wannan tsarin ne don magance yadda gwamnonin jihohi suke nada kwamitocin rikon kwarya ko kuma masu kula da ayyukan kananan hukumomi ba tare da yin zabe ba.
A yanzu haka dai, CBN ya bukaci dukkan kananan hukumomi su mika bayanan asusunsu na tsawan shekaru biyu kafin a fara biyansu.
CBN Ya kuma soma bude asusun banki na kananan hukumomi wanda zai dunga tura musu kudadensu kai tsaye.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp