ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnonin Arewa Sun Kafa Asusun Tallafa Wa Tsaro, Kowace Jiha Za Ta Riƙa Bayar Da Biliyan 1 Duk Wata

by Khalid Idris Doya and Sulaiman
3 weeks ago
Arewa

A ƙoƙarin ƙungiyar gwamnonin Arewa na yaƙi da matsalolin tsaro da suka addabi yankin, gwamnonin sun amince da samar da Asusun Gidauniyar Tsaro na yanki da suka tsara domin samar da wadataccen kuɗaɗe don ƙarfafa ayyukan tsaro a faɗin yankin Arewa.

 

Sun cimma wannan matsayar ne a yayin zaman haɗin guiwa na musamman tsakanin ƙungiyar gwamnonin jihohin Arewan (NSGF) da Majalisar Sarakunan Arewa wanda ya gudana a Sir Kashim Ibrahim House, Kaduna ranar Litinin.

ADVERTISEMENT
  • Sultan Ya Nemi Gwamnonin Arewa Da Su Riƙa Saurarar Masu Sukarsu
  • Sojoji Sun Ceto Mutum 6 Da Aka Sace A Dajin Kogi

Shugaban NSGF kuma Gwamnan jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya shi ne ya jagoranci zaman, wanda aka cimma matsayar cewa kowace jiha daga cikin jihohi 19 da suke faɗin Arewa za su ke bayar da gudunmawar Naira biliyan ɗaya duk wata kuma za a ke cirewa ne kai tsaye bisa tsarin da dukkanin masu ruwa da tsaki suka aminta.

 

LABARAI MASU NASABA

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

Bayan cire kuɗin kai tsaye zai shiga asusun gidauniyar tsaron da aka samar domin yaƙi da matsalar tsaro ciki har da yaƙi da garkuwa da mutane.

 

Gwamnoni da sarakunan sun nuna cewa wannan matakin ya kamata a ɗauke shi tsawon lokaci domin haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen tunƙarar matsalar tsaro da ya addabi yankin tsawon shekaru.

 

A jawabin bayan taro wanda shugaban ƙungiyar gwamnonin arewa Muhammadu Inuwa Yahaya, ya fitar ya ce, asusun gidauniyar kai tsaye zai tafi ne wajen inganta ayyukan hukumomin tsaro, inganta samar da bayanai na sirri, tallafa wa amfani da fasaha a ɓangaren aikin tsaro, da kuma kyautata tsarin kai ɗaukin gaggawa ga al’ummomin da ke cikin buƙatar kai ɗaukin jami’an tsaro a yayin da suke cikin barazana ta tsaro.

 

Sanarwar bayan taron wanda kakakin gwamnan jihar Gombe, Ismaila Uba Misilli ya fitar, ƙungiyar ta miƙa jajenta wa mutane da gwamnatocin jihohin Kebbi, Kwara, Kogi, Neja, Sokoto, Jigawa, da Kano a bisa garkuwa da mutane da aka samu rahoton aukuwar su a cikin jihohin kwanakin baya, tare da jajanta ma waɗanda harin ‘yan ta’addan Boko Haram na baya-bayan nan ya shafa a jihohin Borno da Yobe.

 

Gwamnonin sun jinjina wa yunƙurin gaggawa da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ɗauka wanda hakan ya kai ga samun nasarar ceto ɗaliban da aka yi garkuwa da su tare da azama da yake ƙara sanya wajen yaƙi da matsalar tsaro a faɗin ƙasar nan.

 

A yayin da suke jaddada matsayinsu da suka jima a kai, gwamnonin sun jaddada cikakken goyon bayansu ga kafa rundunar ‘yan sandan jihohi, inda suka buƙaci ‘yan majalisar tarayya da na jihohi daga yankin da su hanzarta aiwatar da duk wani da ake nema domin ganin an sami nasarar wannan batun.

 

Kungiyar ta kuma nuna damuwa kan yadda haƙo ma’adinan ba bisa ƙa’ida ba ke ƙara ta’azzara wajen haifar da rashin tsaro tare da yanke shawarar bai wa shugaba Tinubu shawarar cewa Ministan ma’adinai ya dakatar da duk wani aikin haƙar ma’adinai na tsawon watanni shida. Hakan zai ba da damar gudanar da cikakken bincike da sabunta lasisin haƙar ma’adinai tare da haɗin gwiwar gwamnatocin jihohi.

 

Gwamnonin Arewa da Sarakunan Gargajiya sun amince da muhimmancin haɗin kai, kuma ɗaukar maida hankali kan nauyin da ya rataya a wuyansu wajen tunƙarar ƙalubalen da yankin ke fuskanta.

 

Sun yi alƙawarin ci gaba da yin aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin tsaro, majalisar sarauta da al’umma domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a arewa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta
Manyan Labarai

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tinubu
Manyan Labarai

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani
Manyan Labarai

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Next Post
An Yi Taron Tattaunawa Kan Littafi Na 5 Na Xi Jinping Kan Dabarun Shugabanci A Kenya

An Yi Taron Tattaunawa Kan Littafi Na 5 Na Xi Jinping Kan Dabarun Shugabanci A Kenya

LABARAI MASU NASABA

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.