Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF), ta bayyana damuwarta kan sabon rikici da ya ɓarke a wasu yankunan Jihar Filato, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu.
A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar kuma gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta miƙa ta’aziyyarta ga gwamnatin Filato da iyalan waɗanda abin ya shafa.
- Kamfanonin Lantarki Na Shirin Shiga Yajin Aiki Kan Bashin Naira Tiriliyan 4
- Matashin Da Ya Ƙware Wajen Kashe Mutane Da Ƙwace Ya Miƙa Kansa Ga ‘Yansanda A Kano
Gwamnonin sun bayyana lamarin a matsayin abin baƙin ciki, musamman ganin yadda jihar ke zaune lafiya na wani tsawon wani lokaci, sakamakon ƙoƙarin gwamnati, sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma.
Sun buƙaci shugabannin addini da na al’umma su haɗa kai da Gwamna Caleb Mutfwang don kawo ƙarshen tashin hankali, haɗa kan jama’a da kuma wanzar da zaman lafiya mai ɗorewa a Jihar Filato.
Sun yi tuni cewa mutanen da aka kashe su ne masu ciyar da iyalansu, ginshiƙan danginsu da kuma alfaharinsu.
Sun roƙi a dakatar da duk wani nau’in tashin hankali da ake yi a jihar.
Ƙungiyar ta kuma yi addu’arsamun rahamar Allah ga waɗanda suka rasa rayukansu tare da fatan samun sauki ga waɗanda suka jikkata.
Ta kuma yi kira ga kowa da kowa da ya rungumi zaman lafiya da tattaunawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp