Kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP sun caccaki gwamnatin tarayya kan matsin rayuwa tare da yin kira ta kawo matakan gaggawa da za su kawar da matsalar tattalin arziki da kalubalan tsaro da ke addabar kasar nan.
Shugaban kungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed shi ya yi wannan kira lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala ganawar gwamnonin jam’iyyar adawa da ya gudana a gidan gwamnatin Jihar Oyo da ke Abuja.
- Nijeriya Za Ta Shawo Kan Ƙalubalen Da Take Fuskanta Nan Gaba Kaɗan – Ganduje
- Shugaba Tinubu Ya Gana Da Gwamnoni Kan Ƙalubalen Da Nijeriya Ke Fuskanta
Da yake amsa tambayoyi kan tsadar rayuwa da ake ciki, gwamnan ya bayyana cewa sun goyi bayan cire tallafin man fetur da wannan gwamnati ta yi ne bisa fatan za a samu saukin rayuwa, amma lamarin ba haka yake ba.
Ya bayyana damuwarsa kan yadda darajar naira ke kara zubewa kasa warwar, yayin da ake ci gaba da samun tsadar rayuwa.
A cewarsa, “Lallai muna caccakan munanan manufofin gwamnatin tarayya. Amma a bangare daya kuma, mun goyi bayan wannan gwamnati na cire tallafin mai, saboda muna da tabbacin cewa hakan shi ne manufa, idan har muka hada kai, to za a samu mafita kan wannan lamari.
“Amma muna ganin shi ne ya kawo faduwar daragar naira wanda ya haddasa tsadar rayuwa, inda a yanzu muke kafada da kafada da kasar Benezuela.
Saboda haka, muna hamayya da munanan manufofin gwamnatin tarayya ba tare da mun zagi kowa ba.
“Mun dauki wannan mataki ne domin ceto ‘yan Nijeriya da kuma kasar nan ta yadda za mu yi wasu abubuwa domin taimaka wa kawunanmu.”
Tun da farko, kungiyar ta jaddata manufarta na kirkiran ‘yansandar jihohi a matsayin wani taki da zai kawo karshen matsalar tsaro a Nijeriya.
“Wannan tattaunawar ta shafi sake duba yadda kasa ke ciki da kuma matsin rayuwa da ‘yan Nijeriya suka tsinci kansu a ciki sakamakon matsin tattalin arziki da kalubalan tsaro da kasar ke fuskanta. Wannan kungiyarmu tana kira ga gwamnatin tarayya ta bullo da wasu shirye-shirye da zai kunshi dukkanin gwamnatocin kasar nan domin kawo karshen lamarin.
“Gwamnonin PDP za su ci gaba da yin iya bakin kokarinsu wajen kawo karshen matsalar tsaro domin bayar da kariya ga al’ummar kasar nan. Muna jaddada aniyarmu na yin kira da a kirkiro ‘yansandar jihohi domin kaucewa duk wata hanya ta yin amfani da ofishi ba bisa ka’ida ba ga bangarorin gwamnati.
“Lallain kungiyarmu ta koka kan yadda darajar naira ya karye tare da yinkira ga hukumomin kula da kudade da su ballo da mafita,” in ji kungiyar gwamnonin PDP.
Gwamnonin PDP sun amince da kwamitin gudanarwar jam’iyyar na kasakarkashin jagorancin mukaddasin shugaban jam’iyyar na kasa, Umar Damagum. Haka kuma sun bukaci kwamitin ya kira taron gaggawa na k asa ba da jimawa ba.