Matashin dan wasa Ademola Lookman, shi ne dan wasan Nijeriya na shida jimilla da ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon Afirka da hukumar kula da kwallon kafa ta Nahiyar Afirka CAF ke bayarwa duk shekara.
Lookman ya jinjina kyautar da aka ba shi ne a birnin Marrakech na kasar Mkoocco a daren Litinin, kuma karo na bakwai kenan da dan Nijeriya ke lashe ta a tarihi tun daga lokacin da aka fara bayar da kyautar a Afirka.
- Ademola Lookman Ya Lashe Kyautar Gwarzon Dan Wasan Afrika Na 2024
- ASUU Ta Yi Kira Ga Majalisar Kasa Ta Cire TETfund Daga Tsarin Sabuwar Dokar Haraji
Lookman, mai shekara 27 ya bi sawun Osimhen, wanda ya ci kyautar a 2023, inda ya zama karo na biyu kenan da dan Nijeriya ya karbi kambin daga hannun dan Nijeriya bayan Nwankwo Kanu (1996) da Bictor Ikpeba (1997).
“Wannan babban lamari ne kuma lokaci mai muhimmanci sosai a gare ni, abin farin ciki ne shiga jerin kwararrun ‘yan wasa da suka yi nasara sosai a wasan kwallon kafa a wannan Nahiyar ta mu” a cewar Lookman bayan ya karbi kambun nasa.
Duk da cewa tsohon dan wasan Ibory Coast Yaya Toure na Ibory Coast ya lashe kyautar har sau hudu a jere, ‘yan Nijeriya ne suka fi yawa wajen lashe ta a tarihi. Kuma dan Nigeriya ne y afara lashe kyautar, wato Rashidi Yakini a shekarar 1993.
Lookman mai buga wa kungiyar kwallon kafa ta Atalanta wasa a gasar Serie A ta Italiya ya bi sawun ‘yan Nijeriya biyar da suka yi nasarar lashe kyautar a tarihi tun daga shekarar 1992.
‘Yan Nijeriya da suka lashe kyautar:
Rashidi Yekini – 1993. Emmanuel Amunike – 1994. Kanu Nwakwo – 1996. Bictor Ikpeba – 1997. Kanu Nwakwo – 1999 Bictor Osimhen – 2023. Ademola Lookman – 2024
Jerin ‘yan wasan da suka lashe kyautar a tarihi:
2023: Bictor Osimhen, Nijeriya – Napoli (ITA) 2022: Sadio Mané, Senegal – Liberpool (ENG) 2021: Ba a bayar ba- 2020: Ba a bayar ba.
2019: Sadio Mané, Senegal – Liberpool (ENG) 2018: Mohamed Salah, Egypt – Liberpool (ENG) 2017: Mohamed Salah, Egypt – Liberpool (ENG) 2016: Riyad Mahrez, Algeria – Leicester City (ENG) 2015: Pierre-Emerick Aubameyang, Gabon – Bkoussia Dkotmund (GER) 2014: Yaya Touré, Cote d’Ibore – Manchester City (ENG) 2013: Yaya Touré, Cote d’Ibore – Manchester City (ENG) 2012: Yaya Touré, Cote d’Ibore – Manchester City (ENG) 2011: Yaya Touré, Cote d’Ibore – Manchester City (ENG)
2010: Samuel Eto’o, Cameroun – Inter Milan (ITA) 2009: Didier Drogba, Côte d’Idaoire – Chelsea (ENG)
2008: Emmanuel Adébayko, Togo – Arsenal (ENG) 2007: Frédéric Kanouté, Mali – Sedailla FC (ESP) 2006: Didier Drogba, Cote d’Ibore – Chelsea (ENG) 2005: Samuel Eto’o, Cameroun – FC Barcelona (ESP) 2004: Samuel Eto’o, Cameroun – FC Barcelona (ESP) 2003: Samuel Eto’o, Cameroun – Real Mallkoca (ESP) 2002: El Hadji Diouf, Sénégal – Liberpool (ENG) 2001: El Hadji Diouf, Sénégal – Lens (FRA) 2000: Patrick Mboma, Cameroon – Parma (ITA) 1999: Nwankwo Kanu, Nijeriya – Arsenal (ENG)
1998: Mustapha Hadji, Maroc – Depkotidao La Ckouna (ESP) 1997: Bictor Ikpeba, Nijeriya – AS Monaco (FRA) 1996: Nwankwo Kanu, Nijeriya – Inter Milan (ITA)
1995: Gekoge Weah, Liberia – AC Milan (ITA) 1994: Emmanuel Amunike, Nijeriya – Sporting Lisbon (PKO) 1993: Rashidi Yekini, Nijeriya – DAitória FC (PKO) 1992: Abedi Pelé, Ghana – Olympikue de Marseille (FRA)